El Rufai: Abin da Ya Sa Muka Fito da 'Arewa Tech Fest' Domin Taimakawa Jihohinmu
- Nasir El-Rufai ya fito da shirin Arewa Tech Fest domin ganin yadda zai inganta rayuwar matasan Arewa
- Tsohon gwamnan da mutanensa sun cigaba da aikin da aka fara a lokacin ya na mulkin jihar Kaduna
- Hafiz Bayero wanda ya na cikin manyan yaran Malam El-Rufai shi ne kashin bayan tsarin Arewa Tech Fest
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Nasir El-Rufai ya kaddamar da shirin Arewa Tech Fest domin bunkasa harkar fasaha a jihohin da ke Arewacin Najeriya.
Tsohon gwamnan na Kaduna wanda kuma shi ne shugaban Afri-Venture Capital ya assasa shirin ganin yadda aka bar yankin a baya.
Yadda aka haifi Arewa Tech Fest
A wani bidiyo da M. S Ingawa ya wallafa a X, an ji Malam Nasir El-Rufai a Kano ya na amsa tambaya kan dalilin kafa Arewa Tech Fest.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufai ya bayyana cewa wani na hannun damansa, Hafiz Bayero ne ya kirkiro shawarar a lokacin shi ya na gwamna a Kaduna.
El-Rufai ya cigaba da Arewa Tech Fest
Bayan baris ofis a 2023, sai ya ga bukatar su cigaba da wannan kokari don haka ya hada kai da manyan abokansa irinsu Jimi Lawal.
Malam El-Rufai ya ba da misalin yadda aka yi wa Arewacin Najeriya nisa a bangaren fasaha duk da dinbin mutanen da ke yankin.
A cewarsa yankin ne yake dauke da kusan 60% na mutanen kasar, mutane miliyan 103.
"An bar Arewa a baya" - El-Rufai
Ya ce ko lokacin da shugaban kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg ya zo Najeriya, Legas ya je ba tare da ya kula mutanen Arewa ba.
A karkashin Arewa Tech Fest matasa daga Kaduna da sauran jihohin Arewa za su gabatar da tsarin da suke shi domin su iya samun jari.
Tsohon ministan na birnin tarayya Abuja ya kara da cewa daga cikin wadanda aka ba jari, akwai wadanda kasuwancinsu ya mike a yau.
Sanannen abu ne cewa kimanin 90% na kasuwancin da ake farawa ba su kai labari, El-Rufai ya ce wadanda suka dace ne ke yin suna.
Matsalar durkushewar Naira a yau
Ana da labari cewa daga lokacin da sabon gwamnan babban bankin ya shiga ofis zuwa yanzu, Naira ta rasa rabin darajarta a kasuwa.
Duk da asusun kudin kasar waje ya na karuwa a karkashin Yemi Cordoso, Naira kara yin kasa ta ke yi, yanzu ta zarce N1700 daga N700.
Asali: Legit.ng