Yadda Aka Sulale da Bobrisky daga Kurkuku, Ya yi makonni 3 Maimakon Watanni 6

Yadda Aka Sulale da Bobrisky daga Kurkuku, Ya yi makonni 3 Maimakon Watanni 6

  • Bayan samun shi da laifin cin mutuncin Naira, kotu ta yankewa Okuneye Idris Olanrewaju hukuncin daurin watanni
  • A maimakon ya yi watanni shida a gidan gyaran hali, ana zargin bayan wasu ‘yan kwanaki kadan aka fito da shi daga kaso
  • Wani bincike ya yi ikirarin ba a dade ba aka dauke Okuneye Idris Olanrewaju daga Kirkiri da ya biya cin hancin tulin kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Kwanaki ne aka yankewa Okuneye Idris Olanrewaju watau Bobrisky wanda ya yi fice a harkar daudu hukuncin daurin watanni shida.

Kotu ta yankwa Okuneye Idris Olanrewaju hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, sai dai zaman kason na shi ya zo da wasu badakala.

Kara karanta wannan

'Zai kara aure?': Al'umma sun bayyana ra'ayoyi kan sakin Seaman Abbas

Bobrisky
Ana tunanin Bobrisky bai shafe watanni 6 a gidan yari ba Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Bobrisky bai yi watanni 6 a daure ba

Wani bincike da jaridar FIJ ta gudanar ya na zargin cewa Bobrisky bai yi watanni shida a daure ba, makonni uku kurum ya yi a gidan yarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta shaida cewa bayan makonni uku kacal sai aka dauke ‘dan daudun daga gidan gyaran hali, ya bar Kirkiri tun a cikin Agusta.

Ina aka kai Bobrisky daga Kirkiri?

Wadanda suka san wannan mutumi sun nuna cewa an dauke shi zuwa wani boyayyan wuri da ba a sani ba, ya yi ta rayuwa wajen kurkuku.

A cewar majiyar, an biya kudi domin a iya dauke Okuneye Idris Olanrewaju daga gidan gyaran halin na Kirkiri wanda ya shahara a Najeriya.

Bobrisky: An ba 'dan daudu kula a kurkuku

A lokacin da yake tsare, majiyar ta ce an rika ba Bobrisky kulawa ta musamman, ana tsare shi a gidan gyaran halin kamar wani shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yiwa Jonathan martani kan tsige shi daga gwamnan CBN a 2013

Bayan haka, jaridar Sahara Reporters da ta kawo labarin ta ce an warewa ‘dan daudun daki na musamman, aka nesanta shi da daurarru.

Akwai jita-jita cewa wani ‘dan daudun mai suna James Brown ya ziyarci Bobrisky lokacin da ya kamata a ce ya na daure a kurkukun a Legas.

Sai dai babu tabbacin batun ya tabbata, domin wata majiya ta karyata ikirarin, ta ce lokacin da Brown ya je kurkuku, bai hadu da Bobrisky ba.

Rahotanni sun ce zuwa yanzu mahukunta ba su iya cewa komai game da labarin ba duk da an kafa kwamiti da zai yi binciki wasu jami’ai.

Bobrisky ya ba jami'ai cin hanci?

Ana da labari 'dan daudun nan, Idris Okuneye ya zargi jami'an hukumar gidajen yari da kuma na EFCC da karbar cin hanci daga hannunsa.

Ana zargin Bobrisky ya bayyana haka ne a cikin wata murya da aka yi ta yadawa hakan ta sa Ministan cikin gida, ya ce a yi bincike a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng