Shugaban Kamfanin BUA Ya Tona Masu Jawo Tsadar Kaya da Karfi da Yaji a Kasuwa

Shugaban Kamfanin BUA Ya Tona Masu Jawo Tsadar Kaya da Karfi da Yaji a Kasuwa

  • Abdul Samad Rabiu ya zargi abokan harkokinsu da haifar da tsadar kaya ta hanyar tilasta tashin farashi a kasuwa
  • Shugaban kamfanin na BUA Foods PLC ya bayyana yadda kamfanoni ke jin haushin irin araha da saukin kayansu
  • Alhaji Abdul Samad Rabiu ya kawo misalin fulawa wanda ya ce da gan-gan kwanaki aka sa buhu ya kai N70, 000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaban kamfanin BUA Foods Plc, Abdul Samad Rabiu, ya yi maganar karancin kaya da hauhawar farashinsu a Najeriya.

Duk da yunkurin da gwamnati da mutane da-dama su ke yi, har yanzu kaya suna cigaba da tashi, an rasa yadda za a samu sauki.

Alhaji Abdul Samad Rabiu
Shugaban Kamfanin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu ya koka da halin 'yan kasuwa Hoto: www.forbes.com
Asali: UGC

Shugaban BUA ya fadi sharrin 'yan kasuwa

A ranar Alhamis Punch ta ce Alhaji Abdul Samad Rabiu ya tabo wannan batu da yake jawabi a wajen taron kamfaninsa watau BUA.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya magantu kan rigimar matatar Dangote da NNPCL, ya gano masu laifi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana a birnin Abuja, ‘dan kasuwan ya yabawa shugaban kasa watau Bola Tinubu da ya bari a shigo da kayan abinci.

'Yan kasuwar fulawa da kamfanin BUA

Attajirin ya ba da labarin yadda sauran kamfanonin da ke yin fulawa su ka kafe domin ganin buhu ya yi tsadar da ake ta kuka.

"Kayan BUA sun fi kowane araha a kasuwa. Saboda mu na kamfanonin da suke da irin kayanmu, da wahala farashi ya yi kasa.
"Alal misali kwanakin baya buhun fulawa ya kai N70, 000. Sai mu ka bar namu a N50, 000, aka dade domin mu matsawa kamfanoni ya sauka.
"Amma da suka lura haka za a yi, sai suka daina aiki da gan-gan, dole farashi ya tashi sama."

- Alhaji Abdul Samad Rabiu

Shugaban na BUA ya ce dillalai suka rika kara N20, 000 a kan kowane buhunsu, ‘yan kasuwa suka rika samun N20m kan kowace tirela.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun fusata da 'Hamster Kombat', sun yi magana kan kashi na 2

Labarin da aka samu a shafin Reuben Abati ya ce wasu kamfanoni sun ji haushin yadda BUA yake saida kayan shi da araha a kasuwa.

A shekara mai zuwa, an rahoto a shafin X ya cewa abubuwa za su kara yi wa kamfanin BUA kyau a harkar taliya da kuma fulawa.

Mai kamfanin BUA ya ba da N2bn

An ji labari BUA ya tura wakilai su yi jaje ga al'ummar Maiduguri bayan ambaliyar ruwa inda AbdulSamad Rabiu ya ba da tallafin N1bn.

Bayan kudi ya hada da kayan abinci na Naira biliyan ɗaya. Haka nan ya ce zai sake turo tirelolin shinkafa da taliya domin rabawa jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng