CNG: Gwamnatin Tinubu Za Ta Raba Keke Napep 2000 Masu Amfani da Gas

CNG: Gwamnatin Tinubu Za Ta Raba Keke Napep 2000 Masu Amfani da Gas

  • Gwamnatin tarayya na cigaba da shirye-shirye kan bikin zagayowar ranar samun yancin kan Najeriya
  • Daga cikin abubuwan da za a yi akwai rabawa matasa Keke Napep mai amfani da gas samfurin CNG
  • Karamin Ministan cigaban matasa ya ce wannan shi ne karo na farko inda matasa 2,000 za su mora

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce an kammala shirin raba baburin adaidata sahu mai amfani da iskar gas na CNG ga matasan kasar nan 2,000.

Rabon da za a yi shi ta ma'aikatar cigaban matasa ta ce rabon wani bangare ne na bikin cikar Najeriya 64 da samun yancin mulkin kai.

Kara karanta wannan

"Da wuya a magance rashin tsaro:" Obasanjo ya gano abin da ke barazana ga kasa

Tinubu
Gwamnati za ta raba adaidaita sahu ga matasa 2,000 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa karamin Ministan cigaban matasa, Ayodele Olawale ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta rabawa matasa Keke Napep

Karamin Ministan cigaban matasa, Ayodele Olawale ya ce raba babaran masu kafa uku da ke amfani da iskar gas samfurin CNG zai taimaki sana'ar matasa.

Ya ce matasan da za su rabauta da baburan za su rika kashe 20% na abin da su ke kashewa kan fetur a halin yanzu.

Gwamnati za ta cigaba da tallafawa matasa

Gwamnatin tarayya ta ce za matasa 2,000 da za a ba babura masu kafa uku su ne kashi na farko a cikin shirin raba abin hawan don gudunar da sana'a.

Mista Ayodele Olawale ya bayyana cewa ana sa ran masu amfani da baburan za su samu karuwar riba, da rage tsadar sufuri ga fasinjojinsu.

Kara karanta wannan

Bayan zarginta da jefa jama'a a wahala, gwamnati ta fadi alfanun cire tallafin fetur

"Ana taimakon jama'a," cewar gwamnati

A baya kun samu labarin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce tun bayan cire tallafi man fetur ta ke fafutukar taimakawa mazauna kasar nan ka halin da su ka shiga.

Sakataren gwamnati, Sanata George Akume ne ya bayyana haka, ya ce daga cire tallafin zuwa yanzu, an tallafawa mutane akalla 20,000,000 da kudin rage radadi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.