Za a Biya Ma'aikata N930,000 a Shekara? An Fadi Tsarin Biyan Sabon Albashin N70,000

Za a Biya Ma'aikata N930,000 a Shekara? An Fadi Tsarin Biyan Sabon Albashin N70,000

  • Gwamnatin Tarayya ta fitar da jadawalin yadda kowane ma'aikaci zai samu a sabon mafi ƙarancin albashin da aka kawo
  • An kasafta tsarin yadda ma'aikatan gwamnati za mu samu albashi har na tsawon shekara bayan karin kudin da aka yi masu
  • Hakan na zuwa bayan rahotanni sun tabbatar da fara biyan mafi ƙarancin albashi a jiya Alhamis 26 ga watan Satumbar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa an fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin N70,000.

Gwamnatin Tarayya ta fara biyan mafi ƙarancin albashi a jiya Alhamis 26 ga watan Satumbar 2024.

Gwamnatin Tinubu ta fara biyan mai ma'aikata sabon albashi
An fitar da tsarin yadda kowane ma'aikaci zai samu a shekara bayan karin albashi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Gwamnatin Tinubu ta fara biyan sabon albashi

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, Tinubu ya fara biyan ma'aikata sabon albashin N70,000

Punch ta ruwaito yadda aka kasafta abin da kowane ma'aikaci zai samu a shekara daga mataki na daya har na 17.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikata za su samu albashin ne duba da kwarewar aiki da zurfin karatu da kuma yawan matakinsu a aikin.

Kakakin ofishin babban mai kula da kudi na Najeriya, Bawa Mokwa shi ya tabbatar da haka, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Sai dai Mokwa bai bayyana ko za a biya albashin tun daga watannin baya ba kamar yadda aka yi alkawari.

Yadda tsarin biyan albashin zai kasance

An kasafta yadda za a biya ma'aikatan musamman daga mataki na daya zuwa 15 da aka fi ba fifiko.

Ma'aikata da ke mataki na daya za su samu N930,000 a shekara sai mataki na biyu N934,160 sai kuma mataki na uku N937,713.

Mataki na hudu za su tashi da N950,243 sai na biyar N973,123 da mataki na shida N1,041,786 sai kuma mataki na bakwai N1,277,667.

Kara karanta wannan

Dauda vs Matawalle: Gwamnati ta fara binciken masu daukar nauyin 'yan bindiga

Wadanda suke mataki na takwas za su samu N1, 479,276 sai na tara N1, 641,226 da kuma na 10 N1, 806,041.

Daga na 12 za su samu N2,007,152 sai na 13 N2,182,637 sai na 15 N2,358,936 yayin da mataki na 16 za su samu N3,611,689.

Ma'aikata da ke mataki na 17 da suka hada da manyan sakatarori za su samu N6,918,560 a cikin shekara daya.

Tinubu ya magantu kan shigo da abinci

Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa kan yadda ake cigaba da shigo da abinci Najeriya ba kakkautawa.

Gwamnatin ta ce ya kamata a rage yawan shigo da kayan abinci domin samar da wadataccen abinci a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.