Bayan Zarginta da Jefa Jama'a a Wahala, Gwamnati Ta Fadi Alfanun Cire Tallafin Fetur

Bayan Zarginta da Jefa Jama'a a Wahala, Gwamnati Ta Fadi Alfanun Cire Tallafin Fetur

  • Gwamnatin tarayya ta ce an turawa mutane akalla miliyan 20 kudi domin saukaka wahalar rayuwa a yau
  • Bayanin na zuwa yayin da kasar nan ke shirin bikin zagayowar samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka
  • Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya ce akwai dimbin alfanun cire tallafin man fetur ga kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit.Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta taimaki akalla mutane miliyan 20 a kasar nan ta tsare-tsaren da ta fitar domin saukaka wahalar rayuwa.

Sakataren gwamnati, Sanata George Akume ne ya yi ikirarin yayin tattaunawa kan shirin bikin zagayowar ranar samun yancin kasar nan karo na 64.

Kara karanta wannan

Gangamin zanga zangar 1 Oktoba ya kankama, an mika bukatu ga Tinubu

Tinubu
Gwamnati ta ce an taimaki mutum miliyan 20 bayan cire tallafin fetur Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa, Sanato George Akume ya ce an taimakawa yan kasar nan ta shirin aika kudi ta asusun bankinsu kai tsaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta fadi amfanin cire tallafin fetur

Sakataren gwamnati, George Akume ya ce a cire tallafin fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi, ta kara fadada bangaren tare da kawo cigaba.

Ya ce matakin ya kara buda kasuwar ma'adanan ga yan kasuwar ciki da wajen kasar nan wajen zuba jari.

Ya kara da cewa akwai aikace-aikacen hanya da gwamnatin ke yi, kuma za su taimaka wajen habaka kasuwanci.

Gwamnati na jiran kayan abinci daga ketare

Gwamnatin tarayya ta ce shirinta na samar da abinci mai sauki na nan, amma a sa ido kan irin abincin da za a rika shigowa da su ba tare da haraji ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware N24bn domin ragewa talakawa radadi, an fadi yadda tsarin yake

Ministan tattalin arziki, Wale Edun da ya bayyana haka ya ce ana dakon masara da alkaman da za a shigo da su daga ketare, amma ya ce kar a dogara da kayan kasashen waje.

An wanke gwamnati daga cire tallafin fetur

A baya kun ji cewa tsohon shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Yakubu Dogara ya wanke shugaban kasa, Bola Tinubu daga zargin cewa shi ne ya jagoranci cire tallafin fetur.

Hon Yakubu Dogara ya fallasa cewa tun kafin Bola Ahmed Tinubu ya kama ragamar jagorancin kasar nan aka cire tallafin man fetur, shi tabbatarwa kawai ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.