Fetur a Najeriya Ya Zarce na Saudiya Araha da 40%? An Gano Kuskure a Ikirarin Dangote
A ranar 23 ga watan Satumba, Aliko Dangote, wanda ya kafa matatar man Dangote, ya yi ikirarin cewa man fetur ya fi araha da 40% a Najeriya fiye da a kasar Saudiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Aliko Dangote, ya bayyana farashin man fetur a Najeriya a matsayin marar dorewa idan aka kwatanta da sauran kasashe musamman Saudiyya.
Legit Hausa ta gudanar da bincike kan wannan ikirari da Dangote ya yi ta hanyar tattaro bayanin farashin fetur a Najeriya da kuma kasar Saudiya.
"Fetur ya fi arha a Najeriya" - Dangote
Da ya ke magana a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Bloomberg, Dangote ya goyi bayan cire tallafin man fetur a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Alal misali, a kasar Saudiya, ‘yan kasar sun yi imanin cewa man fetur ni'ima ce da Allah ya ba su, kuma bai kamata su saya da tsada ba. Gwamnati ta na sayar masu shi da arha.
"Amma a yau da nake wannan maganar, man fetur ya fi arha da kusan kashi 40% a Najeriya fiye da a Saudiya, wanda a tunanina hakan ba shi da ma'ana."
Dangote ya bayyana cewa nauyin tallafin ya yi matukar nauyi ga gwamnatin Najeriya, yana mai cewa duk kasashen duniya sun cire tallafin man fetur.
Bincike kan ikirarin Dangote
Bayanai daga shafin Saudi Aramco, wani kamfanin mai na Saudiya, sun nuna cewa a watan Satumba farashin litar fetur na octane 95 ya kai riyal 2.33 yayin da na octane 91 ya kai riyal 2.18.
Ya zuwa ranar 25 ga watan Satumba, babban bankin kasar Saudiya ya bayyana cewa, farashin canjin Riyal zuwa Naira ya kai N438.5/1 Riyal.
Hakan na nufin farashin litar man fetur na octane 95 ya kai N1,021.92 yayin da man fetur na octane 91 ya kai N956.14 (a canjin Riyal zuwa Naira)
A gefe guda kuma, a ranar 3 ga Satumba, kamfanin mai na Najeriya (NNPC) ya kara farashin man fetur zuwa N855 a kan kowace lita.
Bayan an canja kudin Riyal zuwa Naira, an yi amfani da darajar Naira wajen tantance bambancin farashin man fetur a kasashen biyu.
Sakamakon haka, man fetur na Saudiya ya fi tsada da 17.78% (na man octane 95) da kuma 11.16% (na man octane 91) a kan farashin man Najeriya.
Haka kuma, canza farashin man fetur na kasashen biyu zuwa dala zai samar da irin wannan sakamako wanda bai kai 40% da Dangote ya yi ikirarin ba.
An gano Dangote ya yi kuskure
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa babu gaskiya a wannan ikirari da Dangote ya yi, duk da cewa ta wata fuskar yana da 'yar gaskiya, inji rahoton The Cable.
Ikirarin cewa farashin man fetur ya fi arha da kashi 40 a Najeriya fiye da na Saudiyya ba daidai ba ne.
Yayin da aka tabbatar da cewa farashin man fetur na Saudiya ya fi tsada a kan na Najeriya, sai dai binciken ya nunabambancin bai kai kashi 40 ba.
"A karasa cire tallafi" - Dangote ga Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Aliko Dangote ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya cire tallafin man fetur gaba daya domin daidaita farashi.
Mai matatar man fetur din ya nuna cewa gwamnatin tarayya ba za ta iya ci gaba da jure biyan tallafi ba don haka yanzu ne lokacin da ya fi dacewa a cire shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng