Hankali ba zai dauka ba ace Saudi ta fi Najeriya arahar man fetur - Buhari
- Muhammadu Buhari ya kare karin a ya y ina kudin man fetur a Najeriya
- Shugaban kasar ya ce bai dace fetur ya fi araha a Najeriya a kan Saudi ba
- Mafi karancin albashin mutanen ya nunka na kasar Najeriya kusan sau 10
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabo maganar karin kudin man fetur a jawabin da yi na bikin cika shekara 60 da samun ‘yancin kai.
Muhammadu Buhari ya na ganin cewa babu hikima ace Najeriya ta na saida man fetur kasa da abin da ake saidawa kasashen da ke makwabtaka.
Mai girma shugaban kasar ya bayyana haka ne a jawabinsa na ranar 1 ga watan Oktoba, 2020.
Buhari ya ce ba zai yiwu gwamnati ta cigaba da rike farashin fetur ba saboda halin da ake ciki.
KU KARANTA: Buhari ya koka game da halin tattali da tsaro
“A game da wannan, tsaida farashin mai a yadda ya ke ba zai yiwu ba. Tun da Gwamnati ta shiga ofis, ta yi la’akari da sauya farashin man fetur.” Inji Buhari.
Shugaban ya kara da cewa: “Amma halin da za a shiga a sakamakon hakan ya yi wa gwamnati nauyi”
“Za a sauya yadda ake saida kayan mai. Yanzu mu na saida litar fetur a kan N161. Idan aka kamanta da makwabtanmu, za a fahimci abin da ake nufi.”
"Chadi, kasa ce mai arzikin mai, ta na saida lita a kan N362. Nijar, ita mai arzikin mai a N346. A Ghana, wata kasa mai arziki, ana saida lita ne a kan N326.”
KU KARANTA: Abubuwan da Buhari ya fada a jawabin bikin 'yancin-kai
Buhari bai tsaya nan ba wajen kare karin da gwamnatinsa ta yi, ya ce a kasashen Masar da Saudi Arabia, litar man fetur ya na tashi ne a kan N211 da N168.
“Babu hankali ace mai ya fi araha a Saudi a kan Najeriya.”
Amma mutane irinsu Bulama Bukarti, sun tunawa shugaban kasar cewa mafi karancin albashi a Saudi ya haura N300, 000, yayin da ake biyan N38, 000 a nan.
A game da tabarbarewar Najeriya, shugaba Muhammau Buhari ya dora laifi a kan gwamnatocin da aka yi a baya na su Obasanjo, Yar'Adua da kuma Jonathan.
Shugaban kasar bai ambaci sunan shugabannin ba, amma ya ce gwamnatocin 1999 zuwa 2015.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng