'Na Janye': Ustaz Abubakar Zariya Ya Gano Kuskure a Fatawar da Ya Bayar kan 'Mining'

'Na Janye': Ustaz Abubakar Zariya Ya Gano Kuskure a Fatawar da Ya Bayar kan 'Mining'

  • Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zariya ya yi magana kan wata fatawa da ya bayar game da halarcin 'mining' na sulallan crypto
  • Malamin ya yi nuni da cewa ya bayar da fatawar ne saboda la'akari da halin matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar Najeriya
  • To sai dai daga baya an ankarar da shi kuskuren amfani da ayar da ya yi a fatawar, inda ya ba da hakuri tare da janye fatawar ayar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A yayin da 'yan baiwa ke cike da jin haushin Hamster Kombat kan rashin darajar da ya yi a kasuwa, Ustaz Abubakar Salihu Zariya ya yi magana kan halaccin 'mining.'

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya shiga matsala, an yi wa layin wayarsa kutse a Najeriya

Ustaz Abubakar Zariya ya ce akwai kuskure a kan yadda ya yi amfani da wata aya wajen ba da fatawar halarcin 'mining' kuma yanzu ya warware wannan fatawa.

Ustaz Abubakar Zariya ya yi magana kan fatawar da ya bayar game da hallacin mining
Ustaz Abubakar Zariya ya janye fatawar ayar da ya bayar a kan halarcin 'mining'. Hoto: Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zaria
Asali: Facebook

Wace fatawa malam ya bayar kan Mining?

A cikin wani faifan bidiyo da malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a kwanakin baya ya ba da fatawar cewa 'mining' ya halatta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkali Abubakar Zariya ya ce a lokacin ya halatta daddanna waya domin tara sulallan crypto saboda halin matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar.

A iya nazarinsa, harkar 'mining' za ta halatta kasancewar masu yi na samun kudi daga ciki wanda zai rufa masu asiri a yanayin da kasar ke ciki.

Malam ya yi kuskure a fatawa

To sai dai malamin ya ce daga bisani ne ya samu kiraye-kiraye daga malamai wadanda suka nuna masa kuskuren amfani da ayar da ya bayar a wannan fatawa.

Kara karanta wannan

Fetur a Najeriya ya zarce na Saudiya araha da 40%? An gano kuskure a ikirarin Dangote

Ustaz Abubakar Zariya ya ce:

"Duba da yanayi na halin kuncin rayuwa da jama'a suke ciki, ina cikin malaman da suka yarda cewa mining halar ne.
"To sai dai kuskurena shi ne na ajiye aya ba a muhallinta ba, domin ayar na magana a kan bashi ni kuma na kawo ta a kan 'mining', wannan kuskuren na karbe shi.
"Fatawata ta ajiye wannan ayar da na yi kuskure ne, na janye. Ina fatan al'umma za su yi mun uzuri kasancewata dan Adam wanda zai iya yin kuskure."

Kalli bidiyon a nan kasa:

Ustaz Abubakar zai kara aure

A wani labarin, mun ruwaito cewa Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zariya ya tabbatar da cewa zai karowa matarsa Hajiya Jamila abokiyar zama.

Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da jita-jitar karin aurensa ta jawo ce-ce-ku-ce la'akari da kambama Jamila da ya ke yawan yi, inda ya ce zai kara auren ba don ya daina sonta ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.