Dauda vs Matawalle: Gwamnati Ta Fara Binciken Masu Daukar Nauyin 'Yan Bindiga

Dauda vs Matawalle: Gwamnati Ta Fara Binciken Masu Daukar Nauyin 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin tarayya ta ce ta soma gudanar da bincike mai zurfi kan zarge-zargen da ake samu na masu daukar nauyin 'yan bindiga
  • Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro, Edward Buba ya ce za a tabbatar an gano masu tallafawa 'yan ta'adda a Arewa maso Yamma
  • Wannan na zuwa ne yayin da Gwamna Dauda Lawal da Bello Matawalle ke zargin juna da daukar nauyin 'yan bindiga a jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hedikwatar tsaro ta ce an fara gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake samu na masu tallafawa ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Daraktan yada labarai na hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron manema labarai a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu manyan jami’an gidan yari 4, ta fadi dalili

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan zarge-zargen daukar nauyin 'yan bindiga a Arewa
Gwamnatin tarayya ta soma bincike kan zarge-zargen masu daukar nauyin ta'addanci a Arewa. Hoto: @daudalawal_, @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

Manjo Janar Buba ya tabbatar da cewa hukumomin da ke da alhakin gudanar da irin wannan aiki sun dukufa ainun domin gano bakin zaren, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zarge-zargen daukar nauyin ta'addanci

An rahoto cewa an soma binciken ne biyo bayan musayar zarge-zarge da aka samu tsakanin ministan tsaro, Bello Matawalle da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.

A ranar Talata, Matawalle ya kalubalanci Dauda Lawal da ya rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba shi da hannu a daukar nauyin ‘yan bindiga

Da ya ke mayar da martani, gwamnan ya sha alwashin fitar da hujjoji kan tuhumar da ya ke yi wa ministan, ya kuma kara da cewa ya kai rahoto ga ofishin Nuhu Ribadu (NSA).

Da aka tambaye shi game da rawar da sojoji suka taka game da zarge-zargen da suka shafi manyan 'yan kasar biyu, kakakin hedikwar tsaorn, Buba, ya ce ana bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

"Na rantse da Kur'ani kan zargin ta'addancin Zamfara:" Matawalle ya yi martani

Jami'an tsaro za su gano bakin zaren

Jaridar The Guardian ta rahoto Manjo Janar Buba na cewa:

"Ina mai tabbatar muku da cewa hukumomin da abin ya shafa kuma aka dorawa alhakin gudanar da bincike kan lamarin na aiki tukuru domin gano bakin zaren."
"A game da abin da ke faruwa kan zarge zargen daukar nauyin 'yan bindiga, nan gaba kadan za ku samu sababbin bayanai domin ana kan yin bincike mai zurfi."

Duk da haka, Manjo Janar Buba ya ce sojojin sun mayar da hankali ne wajen samun nasara a yakin da suke da ‘yan bindiga, kuma sun dukufa wajen ruguza 'yan ta'addan.

"Dalilin sulhu da 'yan bindiga" - Matawalle

A wani labarin, mun ruwaito cewa ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana dalilin da ya sa ya yi sulhu da 'yan bindiga a lokacin da ya ke kan kujerar gwamnan jihar Zamfara.

Bello Matawalle ya yi nuni da cewa ya yi sulhu da 'yan bindigar ne da zuciya daya domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.