Litar Fetur Ta Koma N2500 bayan An Fusata 'Yan Kasuwa, Gwamnati Ta Dauki Mataki

Litar Fetur Ta Koma N2500 bayan An Fusata 'Yan Kasuwa, Gwamnati Ta Dauki Mataki

  • Litar fetur a Akwa Ibom ta tashi zuwa N2,500 biyo bayan kwace motocin 'yan IPMAN da rundunar Operation Delta Safe ta yi a jihar
  • Saboda haka Umo Eno, gwamnan Akwa Ibom, ya dauki wani babban mataki na kafa kwamitin mutane 13 da zai magance rikicin
  • An dorawa kwamitin wanda ya hada da ‘yan kungiyar IPMAN alhakin magance matsalar man fetur a jihar tare fatan farashi zai sauko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Akwa Ibom - Rahotanni sun bayyana cewa farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a jihar Akwa Ibom inda a yanzu ake sayar da lita daya a kan N2500.

Gwamnan jihar, Umo Eno ya kafa kwamitin mutane 13 (PPMC) domin magance matsalar man fetur da ake fama da shi a fadin jiharsa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kaɗu da tashin fetur, ya ba da umarnin sauko da kudin lita daga N2500

Gwamnan Akwa Ibom ya dauki mataki yayin da fetur ya kai N2500 a jiharsa
Gwamnatin Akwa Ibom ta kafa kwamitin magance matsalar fetur yayin da lita ta kai N2500. Hoto: Getty Images
Asali: UGC

An kafa kwamiti kan tsadar man fetur

Kwamitin wanda tsohon dan majalisa Godwin Ekpo ke jagoranta, na da burin magance karancin man fetur da kuma ayyukan ha'inci a gidajen mai, a cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan kwamitin sun hada da wakilai daga ma'aikatu daban-daban, kungiyar kwadago ta Najeriya, da kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN).

Rikicin man fetur ya fara ne a lokacin da kungiyar IPMAN ta umurci 'ya'yanta da su rufe gidajen mai saboda zargin kwace tankokin mansu da rundunar Operation Delta Safe ta yi.

Hakan ya haifar da tashin farashin man fetur ziwa N2,500 a kan kowace lita da kuma nunka farashin sufuri sau uku.

NLC na shirin yajin aiki a Akwa Ibom

Rikicin ya sa kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta nemi ma'aikata da su shirya shiga yajin aiki saboda yadda ma’aikata ke kara shan wahala a jihar.

Kara karanta wannan

Fargabar barkewar rikici a Edo: 'Yan sanda sun dauki matakai bayan nasarar APC

Domin hana hakan ta faru ne aka ce gwamnan jihar ya gaggauta kafa kwamitin PPMC domin warware rikicin tare da fatan lamura za su daidaita.

An shirya kaddamar da kwamitin na PPMC a ranar 27 ga watan Satumba, wanda ke nuna kyakkyawan mataki na magance matsalar man fetur a Akwa Ibom.

Fetur: Majalisa ta ba Tinubu shawara

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta yi magana kan tsadar farashin man fetur da ake fama da ita a kasar nan inda ta ba Shugaba Bola Tinubu shawara.

Kungiyar 'yan majalisu marasa rinjaye a majalisar wakilan ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta rage farashin man fetur domin hana ci gaba da shan wahala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.