Matasan APC Sun Fadi Ministan da Tinubu Ya Kamata Ya Dakatar, Sun Fadi Dalili

Matasan APC Sun Fadi Ministan da Tinubu Ya Kamata Ya Dakatar, Sun Fadi Dalili

  • Wata ƙungiya a jam'iyyar APC ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Bello Matawalle daga muƙaminsa
  • Ƙungiyar TYN ta shawarci Tinubu ya dakatar da ƙaramin ministan tsaron domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi masa
  • ƘTYN ta nuna damuwar cewar rashin bincikar ministan zai ɓata sunan APC da gwamnatin Shugaba Tinubu a idanun 'yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wata ƙungiya a jam’iyyar APC ta Tinubu Youth Network (TYN), ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya daƙatar da ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Kungiyar ta kuma buƙaci shugaban ƙasan da ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan alaƙar Matawalle da ƴan bindiga.

Matasan APC na son a dakatar da Matawalle
Matasan APC sun bukaci Tinubu ya dakatar da Matawalle Hoto: @DOlusegun, @BelloMatawalle1
Asali: Twitter

Da yake magana a wani taron manema labarai a Kaduna ranar Alhamis, babban sakataren TYN, Yusuf Muhammad, ya ce zargin da ake yi wa Matawalle na buƙatar a gudanar da bincike cikin gaggawa, cewar rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Zaben kananan hukumomin Kano: Kotu ta dauki mataki kan bukatar jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ake so Tinubu ya dakatar da Matawalle?

Ƙungiyar ta buƙaci ministan ya yi murabus domin a gudanar da bincike mai zurfi, inda ta ƙara da cewa yin watsi da zargin zai cutar da jam’iyyar APC, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Waɗannan batutuwan sun haɗa da zargin daukar nauyin ƴan bindiga da karkatar da kudaden jihar Zamfara."
"Waɗannan abubuwa ne masu matukar muhimmanci da suka shafi harkokin mulki, tsaro, da jin dadin al’ummar jihar Zamfara, kuma bai kamata a yi wasa da su ba."
"Muna kallon hakan a matsayin wani nauyi da ya rataya a wuyanmu a matsayinmu na matasa mu nemi a yi cikakken bincike kan waɗannan munanan zarge-zarge domin tabbatar da gaskiyar jam’iyyarmu da mai girma Shugaba Tinubu."

- Yusuf Muhammad

Yusuf Muhammad ya buƙaci Tinubu da ka da ya yi watsi da zargin da ake yiwa Matawalle, inda ya ƙara da cewa waɗannan zarge-zargen za su iya ɓata gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Kungiyar NLC ta tsunduma yajin aiki, an samu bayanai

Karanta wasu labaran kan Matawalle

Kungiya ta bayyana dalilin gwamnan Zamfara na tsoron Bello Matawalle

Dattawan Zamfara sun ba Gwamna Dauda shawara kan Matawalle

Daukar nauyin 'yan bindiga: Gwamna Dauda ya dauki mataki kan Matawalle

Matawalle ya yi wa Gwamna Dauda martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi martani kan zargin ɗaukar nauyin ƴan bindiga a Zamfara.

Matawalle ya musanta zargin da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi masa kan cewa shi ne ke ɗaukar nauyin ƴan bindiga a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng