Majalisa Ta Yiwa Tinubu Gata, Ta Amince da Nadin Sabuwar Kwamishiniya a NPC
- Majalisar dattawa ta yi wa Shugaba Bola Tinubu gata da ta amince da bukatarsa ta nada sabuwar kwamishiniya a hukumar kidaya
- Majalisar ta amince da nadin Olukemi Victoria Iyantan a matsayin sabuwar kwamishiniya a NPC a ranar Alhamis, 26 ga Satumba
- Amincewa da nadin Misis Iyantan ya biyo bayan rahoton binciken da kwamitin kidaya da katin dan kasa na majalisar ya gabatar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar dattawa ta amince da nadin Misis Olukemi Victoria Iyantan a matsayin sabuwar kwamishiniya a hukumar kidaya ta kasa (NPC).
An rahoto cewa Misis Iyantan, da majalisar ta amince da nadinta a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba za ta wakilci jihar Ondo a hukumar NPC.
Majalisar dattawa ta yi wa Tinubu gata
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya mika sunan Misis Iyantan ga majalisar dattawan domin tantancewa da kuma amincewa da nadinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amincewa da nadin Misis Iyantan ya biyo bayan rahoton da kwamitin kidaya da katin dan kasa na majalisar ya gabatar karkashin Sanata Abdul Ningi (PDP - Bauchi.)
Kwamitin ya bayyana cewa ya gabatar da bukatar amincewa da nadin Iyantan ga majalisar ne bayan nazarin takardunta da kwamitin ya samu.
Majalisa ta amince da nadin Iyantan a NPC
Hakazalika, kwamitin ya ce Iyantan ta cancanci rike wannan mukami saboda kokarin da ta nuna a aikin gwamnati don haka ta nemi a amince da nadinta, inji Premium Times.
Sanatoci sun amince da shawarar kwamitin a lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin wanda ya jagoranci zaman majalisar ya bukaci a kada kuri’a.
Bayan tabbatar da hakan, Sanata Barau ya bukaci Iyantan da ta hada karfi da karfe da sauran kwamishinoni da shugaban NPC domin ciyar da hukumar gaba.
Tinubu ya kunyata majalisar tarayya
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ce ba zai rattaba hannu kan kudurin tsawaita wa'adin ritayar ma'aikatan majalisar tarayya ba.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana hakan a yayin da ya ke karanta wasikar da Tinubu ya aikawa majalisar a makon nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng