Yadda Dakarun Sojoji Suka Hallaka Shugabannin 'Yan Ta'adda 65

Yadda Dakarun Sojoji Suka Hallaka Shugabannin 'Yan Ta'adda 65

  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana nasarorin da dakarun sojoji suka samu a tsakanin watannin Yuli zuwa Satumban 2024
  • DHQ ta bayyana cewa sojojin sun hallaka ƴan ta'adda ciki har da shugabanninsu guda 65 a yayin artabu daban-daban a sassan ƙasar nan
  • Dakarun sojojin sun kuma cafke mutane 2,782 da ake zargi da ta'addanci tare da kuɓutar da mutane 1,854 da aka yi garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojoji sun hallaka ƴan ta'adda 1,937 a tsakanin watannin Yuli zuwa Satumban 2024.

DHQ ta ƙara da cewa an cafke mutane 2,782 da ake zargi tare da ceto wasu mutane 1,854 da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Naira ta ƙara rikitowa ƙasa, Dala ta kuma tashi a kasuwar canji a Najeriya

Sojoji sun hallaka shugabannin 'yan ta'adda
Sojoji sun hallaka shugabannin 'yan ta'adda 65 Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: UGC

Sojoji sun hallaka shugabannin ƴan ta'adda

Hedkwatar tsaron ta ƙara da cewa daga cikin ƴan ta'addan da aka hallaka akwai shugabanninsu har guda 65, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Jerin ƴan ta'addan da aka kashe

Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa daga cikin shugabannin ƴan ta'addan da aka hallaka akwai, Munzir Arika, Sani Dilla (Dan Hausawan Jubillaram), Ameer Modu, Matawal Bitrus, Thomas Benedict, Mohammed Sani.

Sauran sun haɗa da Rimamy (aka Omo), Terkimbi Injoko da Jacob Uzege, Ibn Kasir, Kachalla Dan Baleri, Kachallah Halilu (Buzu), Kachalla Dan Ali Garin Fadama, Kachalla Basiru Zakarriya da Ofem Emmanuel Igwe.

Ya kuma ƙara da cewa dakarun sojojin sun ƙwato makamai guda 1,304 da alburusai guda 43,347

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta ba zabaɓben gwamnan jihar Edo takarda shaida, bayanai sun fito

Sojoji sun cafke miyagu

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na 'Operation Whirl Stroke' sun cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ƙaramar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.

Sojojin sun cafke mutanen ne tare ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da alburusai a wani samame da suka kai a ranar, 16 ga watan Satumban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng