Talauci: Gwamnati Ta Kara ba Yan Kasa Hakuri, Minista Ya Ce Sauki na Tafe

Talauci: Gwamnati Ta Kara ba Yan Kasa Hakuri, Minista Ya Ce Sauki na Tafe

  • Gwamnatin tarayya ta jaddada matsayarta kan cewa yan kasar nan za su samu saukin rayuwa nan gaba kadan
  • Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ya fadi haka a taron shirin bikin zagayowar samun yanci
  • A ranar 1 Oktoba, 2024 ne kasar nan za ta cika shekaru 64 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta sake ba yan Najeriya hakuri kan halin kunci da wasu daga cikin manufofinta su ka tsunduma jama'a.

Wannan ba shi ne karo na farko da jami'an gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke neman yan kasar nan su yi hakuri da yadda ake tafiyar da tattalin arziki ba.

Kara karanta wannan

"Sai an sake zama:" Sanatan APC ya nemi Tinubu ya kira taron gaggawa kan tattali

Bola Tinubu
Minista ya kara ba yan Najeriya hakuri kan matsin rayuwa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa a wanna karon, Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ne ya nemi a yi hakurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A kara hakuri da Tinubu:" Minista

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce a kara hakuri domin za a mori shirin da shugaban kasa, Bola Tinubu ke yi wa yan kasar nan.

Ya bayyana haka ne a taron shirye-shirye kan bikin zagayowar ranar samun yanci kan kasa bayan ta samu shekaru 64 da samun yancin kai.

Matakin da Tinubu ke dauka kan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce akwai shirin da ta ke yi wajen dora kasar nan a gwadaben ci gaba ta hanyar sake fasalta tattalin arzikin karkara.

Alkawarin na zuwa ne yayin da yan kasar nan ke kokawa kan halin matsi saboda tsadar rayuwa da ake ganin cire tallafin man fetur ne ya jawo.

Kara karanta wannan

Unga79: Shugaba Tinubu ya koda Najeriya, ya ce Afrika ba ta bukatar tallafi daga kasashe

Talauci: Masoyin Tinubu ya ba da hakuri

A baya mun ruwaito cewa wani dan jam'iyyar APC a jihar Osun, Olatubosun Oyintiloye ya ba yan kasar nan hakuri kan yadda ake samun hauhawar farashi da tsadar kaya.

Hon. Olatubosun Oyintiloye na ganin matakin cire tallafin fetur da sauran matakan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za su dora kasar nan kan hanya mai bullewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.