Gwamna Ya yi Albishir, za a Zaga Jihohin Arewa Domin Shirin Fasahar Zamani
- Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sanarwar karbar baƙuncin shirin kimiyya da fasaha na Arewa TECHfest na shekarar 2025
- Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta karbi baƙuncin shirin na shekarar 2024
- Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa shirin Arewa TECHfest zai zaga dukkan jihohin Arewacin Najeriya da kuma Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Gwamantin jihar Katsina ta ce ta shirya tsaf domin karɓar baƙuncin shirin kimiyya da fasaha na Arewa TECHfest a shekarar 2025.
Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Kano ta karbi baƙuncin shirin wanda tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu suka jagoranta.
Hadimin gwamna Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook cewa shirin zai zaga dukkan jihohin Arewacin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a yi shirin Arewa TECHfest a jihohi
Bayan kammala shirin kimiyya da fasaha na Arewa TECHfest a jihar Kano, gwamna Dikko Radda ya ce za a zaga dukkan jihohin Arewacin Najeriya.
Ana gudanar da shirin ne domin farfaɗo da harkokin kimiyya da fasaha da samar da tsare tsare da za su tafi da zamani.
Za a yi taron Arewa TECHfest a Katsina
Bayan kammalawa a jihar Kano, Malam Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa jihar Katsina ce za ta karbi baƙuncin shirin a shekarar 2025.
Gwamna jihar, Dikko Umaru Radda ya ce jihar Katsina za ta karbi baƙuncin shirin hannu biyu-biyu.
Katsina na shirin karbar Arewa TECHfest
Daraktan KATDICT a Katsina, Naufal Ahmed ya ce sun fara shirye-shirye domin gudanar da shirin cikin nasara.
Naufal Ahmed ya kara da cewa kawo shirin Katsina ya dace da manufofin gwamna Dikko Radda na farfaɗo da kimiyya da fasaha a jihar.
Bikin cika shekaru 37 a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa a ranar 23 ga watan Satumba, jihar Katsina ta cika shekaru 37 da kafuwa bayan da Janar Ibrahim Babangida ya cire ta daga Kaduna.
Gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Radda ta bayyana shirye-shiryen da ta ke yi na gudanar da bikin murnar cika shekaru 37.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng