Kimiyya da fasaha: Wani matashi injiniya daga Arewa ya kera sabon na’urar Inverter (Hotuna)
- Wani matashi daga arewa ya kera na’urar inverter wanda ba taba yin irin ta ba a Najeriya
- Na’urar nada karfin rike wutar lantarki wanda za a iya amfani da ita a lokacin da babu wuta
- Ana sa ran kerar wannan na’urar zai sa kudin inverter ta ragu a Najeriya
Wani matashi kuma injiniya daga arrewacin Najeriya mai suna Ahmad Lawal Jari ya kera na’urar inverter wanda za a sayar a nan kasar don taimakawa al’umma Najeriya da kuma inganta tattalin arzikin kasar.
Injiniya Ahmad Lawal Jari wanda kuma cikkeken dan asalin jihar Kano ya kera wanna na’urar ne domin ‘yan Najeriya su amfana da ita.
A Najeriya dai kamar yadda aka sani cewa babu isashen wutar lantarki, hakan yasa wannan matashin ya kera na’urar. Wutar lantarki wani abu ne mai muhimmanci ba ga masu arziki kawai ba ko mutanen birane har da talakawa na bukatar wutar lantarki a kowane lokaci domin gudanar da kasuwanci na yau da kullum.
KU KARANTA: Kwalejin yansanda ta dakatda kurata biyar
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, na’urar a halin yanzu a Najeriya ana sayar da su da tsada saboda mafi yawansu ana shigo da su cikin kasar ne daga kasashen waje, amma yanzu haka da injiniya Lawal Jari ya kera na'urar a nan gida, ana sa ran kudin inverter zai ragu sosai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng