Bayan Fara Aikin Matatarsa: Dangote Ya Samu Kwangilar N158bn daga Gwamnatin Tinubu
- Rahotanni sun ce majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince a ba rukunin kamfanonin Dangote kwangilar Naira biliyan 158
- Dangote zai gina hanyoyin zirga-zirga na tashar ruwa ta Lekki Deep Sea kuma aikin zai karasa har kan titin Shagamu-Benin
- Kwangilar dai wani shiri ne na asusun bunkasa ababen more rayuwa na gwamnatin tarayya da tsarin ba da harajin RITCS
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A wani yunkuri na bunkasa ababen more rayuwa a Najeriya, majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kashe N158bn domin gina titin tashar ruwa ta Lekki Deep Sea.
Wannan aikin zai ratsa ta Epe zuwa babbar hanyar Shagamu-Benin, daya daga cikin manyan hanyoyin sufuri na kasar nan.
Gwamnati ta ba Dangote aikin N158bn
Bayo Onanuga, mai ba da shawara na musamman kan yada labarai da dabaru ga Shugaba Tinubu, ne ya sanar da hakan a shafinsa na X, yana mai cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Majalisar ta amince da kwangilar Naira biliyan 158 domin gina hanyoyin zirga-zirga na tashar ruwa ta Lekki Deep Sea wanda zai bi ta hanyar Epe zuwa Shagamu zuwa Benin.
Za a bai wa kamfanin Dangote kwangilar ne a karkashin asusun bunkasa ababen more rayuwa na gwamnatin tarayya da kuma tsarin ba da harajin RITCS."
Majalisar FEC ta magantu kan haraji
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"Majalisar ta kuma amince da kudurin dokar daidaita tattali, bayan shawarar da kwamitin shugaban kasa kan sake fasalin haraji da kasafi ya bayar.
"Kudurin na neman a sabunta dokokin harajin kasar, inganta fitar da kayayyaki zuwa waje, daidata canji kudi da dai sauran abubuwan da suka shafi tattali."
Ɗaya daga cikin dokokin na ba da sassaucin haraji ga kamfanonin da ke samar da ƙarin aikin yi. Akwai wanda kuma ta ke bayar da sassaucin kudin shiga ga mutane masu zaman kansu."
Aikin tituna zai lakume N2trn
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa majalisar tarayya ta amince da bukatar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta ƙara N6.2trn a kasafin kuɗin 2024 bayan tsallake karatu na uku.
Bayanan da ke cikin kudirin sun nuna cewa Gwamnatin tarayya za ta kashe kusan N2tn a aikin gina titin Legas zuwa Kalaba da wasu ayyukan tituna a faɗin ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng