Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana Fannin da Zai Fi Samun Fifiko a Kasafin Shekarar 2025

Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana Fannin da Zai Fi Samun Fifiko a Kasafin Shekarar 2025

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fara tsara kasafin shekarar 2025 wanda ta ke da yakinin cewa zai yi daidai da muradun 'yan Najeriya
  • Daraktan ofishin kasafin gwamnatin tarayya, Tanimu Yakubu ya bayyana hakan inda ya ce tsaro zai samu fifiko a kasafin na badi
  • Duk da cewa ofishin kasafin na fuskantar kalubale, Tanimu Yakubu ya jaddada cewa 'yan Najeriya za su gamsu da kasafin 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tsaro shi ne a sahun gaba na fannonin da za ta fi mayar da hankali a kansu yayin tsara kasafin shekarar 2025.

Daraktan ofishin kasafin gwamnatin tarayya, Mista Tanimu Yakubu ya bayyana hakan a wani taron jami'an kasafi da aka gudanar a a Abuja a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Murna za ta koma ciki: Kungiyar APC na shirin daukaka kara kan nasarar Ganduje

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan kasafin shekarar 2025
Gwamnarin Bola Tinubu ta fara shirya kasafin 2024, tsaro zai samu fifiko. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ana tsara kasafin 2025 ne ta hanyar amfani da tsarin GIFMIS/BPS na dukkanin ma'aikatu, hukumomi da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsaro zai samu tagomashi a kasafin 2025

Mista Tanimu ya ce gwamnatin Tinubu za ta ba da fifiko kan tsaro domin samar da yanayi mai kyau na tara kudaden shigar kasar a cikin kasafin kudin shekarar 2025.

A cewarsa:

"An dade ana nuna damuwa kan kasafin kudin kasar, masu ruwa da tsaki da dama na son jin ba'asi kan manufofi da kuma yadda aka gudanar da kasafin kudin.
"Dole ne fifikonmu ya kasance kan tsaro domin samar da jari mai yawa, cimma burin masu zuba jari ba tare da nuna son kai ba da kuma karfafawa 'yan kasarmu ."

Gwamnati ta fara shirya kasafin 2025

Yakubu ya bayyana cewa, tun bayan hawansa mulki a watan Yuni, ya fuskanci kalubale wajen sarrafa albarkatu da tsara kasafin kasafin kasar, inji rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Bayan fara aikin matatarsa: Dangote ya samu kwangilar N158bn daga gwamnatin Tinubu

"Horon na yau ya na wakiltar wani muhimmin mataki na magance wadannan kalubale da kuma tabbatar da cewa kasafin kudin 2025 ya yi daidai da muradun 'yan Najeriya.
“Yayin da muke shirya kasafin kudin shekarar 2025, za mu tabbatar mun mayar da hankali kan manufofin jama'a da na gwamnati musamman kan tsaro da ci gaba."

- A cewar daraktan ofishin kasafin.

Tinubu ya kara kasafin kudin 2024

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya mikawa majalisar tarayya bukatarsa na kara Naira tiriliyan 6.2 a kasafin kudin 2024.

Bukatar na kunshe cikin wasikar da shugaban ya aika majalisa wanda Godswill Akpabio ya karanta, inda ake neman karin a kan Naira Tiriliyan 27.5 na kasafin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.