Kano, Katsina: Jerin Jihohi 15 da Za a Kwashe Kwanaki 5 Ana Zabga Ruwa da Iska
- Gwamnatin tarayya ta yi hasashen cewa za a zabga mamakon ruwa a jihohi 15 kuma za a iya samun ambaliya daga 24 zuwa 28 ga Satumba
- Cibiyar ba da sanarwar gaggawa kan ambaliyar ruwa ta kasa (FEWS) ta fitar da hasashen a ranar Talata kamar yadda rahoto ya nuna
- A yayin da cibiyar ta bukaci masu ruwa da tsaki da su kara sanya ido, FEWS ta kuma lissafa jihohin tare da garuruwan da abin zai shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi hasashen cewa za a zabga ruwan sama kamar da bakin kwarya a wurare 35 da ke cikin jihohi 15 na kasar nan.
Cibiyar ba da sanarwar gaggawa kan ambaliyar ruwa ta Kasa (FEWS) da ke karkashin ma'aikatar muhalli ta tarayya ce ta fitar da hasashen a ranar Talata.
Za a zabga ruwa na kwanaki 5
Hasashen ya nuna cewa, jihohin da aka gano da kewayensu na iya fuskantar mamakon ruwan sama wanda zai iya haifar da ambaliya, inji rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cibiyar FEWS ta yi hasashen cewa za a zabga ruwan ne tare da iska daga ranar Litinin 24 ga watan Satumba zuwa ranar 28 ga Satumbar 2024.
Cibiyar ta bukaci masu ruwa da tsaki da su sanya ido sosai kan yanayin ruwan da za a sheka a kwanakin nan domin daukar matakin gaggawa.
Jihohin da za a zabga ruwan
- Delta (Abraka, Agbor, Okpo-Krika, Umukwata, Umugboma, Aboh)
- Edo (Ekpoma, Auchi, Irrua, Ilushi, Sabongidda-Ora, Uromi)
- Taraba (Gembu)
- Kwara (Ilorin)
- Kaduna (Kauru)
- Kebbi (Ribah)
- Zamfara (Majara)
- Neja (Mashegu, Kontagora, Lapai, Rijau, Sarkin-Pawa).
- Katsina (Bindawa, Daura, Funtua, Bakori)
- Nasarawa (Ado, Aso, Mararaba)
- Adamawa (Demsa)
- Jigawa (Gwaram)
- Kogi (Ibaji)
- Kano (Kunchi/Gari, Sumaila)
- Gombe (Nafada)
NiMet: Za a zabga ruwa a Arewa
A wani labarin makamancin wannan, hukumar da ke hasashen yanayi a Najeriya (NiMet) ta bayyana cewa za a iya samun kwarya kwaryan ruwan sama a jihohi 17 na Arewa.
Mun ruwaito hukumar ta sanar da cewa akwai jihohin da ruwan zai yi karbi yayin da wasu jihohin ba zai yi karfi ba amma dai za a iya kwashe kwanaki uku ana tafka shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng