Daukar Nauyin 'Yan Bindiga: Gwamna Dauda Ya Dauki Mataki kan Matawalle

Daukar Nauyin 'Yan Bindiga: Gwamna Dauda Ya Dauki Mataki kan Matawalle

  • Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya sanar da shugaban ƙasa zarge-zargen da ake yi kan Bello Matawalle na ɗaukar nauyin ƴan bindiga
  • Dauda Lawal ya bayyana cewa ya gabatar da hujjoji ga shugaban ƙasan kan zarge-zargen da ake yiwa ƙaramin ministan tsaron ƙasar
  • Ya kuma sha alwashin cewa nan ba da jimawa ba zai gabatarwa duniya hujjojin da yake da su kan tsohon gwamnan na Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Shugaba Bola Tinubu, suna sane da zargin da ake yi wa Bello Matawalle na alaƙa da bindiga.

Gwamna Dauda ya ƙara da cewa ya kai rahoton ministan ga NSA da shugaban ƙasa tare da gabatar musu da wasu hujjoji.

Kara karanta wannan

Ana raɗe raɗin gwamna na shirin sauya sheƙa, ciyamomi sun fice daga jam'iyyar PDP

Dauda ya yiwa Matawalle martani
Gwamna Dauda ya kai karar Matawalle ga Tinubu Hoto: Dauda Lawal, Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

Hakan na zuwa ne bayan ƙaramin ministan tsaron ya fito ya nesanta kansa da hannu kan ayyukan ƴan bindiga a jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Dauda ya ƙaryata Matawalle

Sai dai a wata hira da jaridar The Punch a a ranar Talata, babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Zamfara, Sulaiman Idris, ya ce Matawalle ƙarya yake yi.

Ya kuma sha alwashin cewa nan ba da daɗewa ba za a fitar da dukkanin hujjojin da ake da su a kansa ga manema labarai.

Sulaiman Idris ya ce maigidan nasa wanda a halin yanzu baya ƙasar nan, ya rantse da Alkur’ani, kuma ya yi addu’a cewa Allah Ya hukunta duk wanda ke da hannu a ayyukan ƴan bindiga a jihar.

"Ya aikata hakan (Yin rantsuwa da Alkur’ani). Akwai wani faifan bidiyo nasa a yayin wani taro, lokacin da yake kokawa kan wani lamari da ya faru."

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga taron FEC ana rade raɗin za a kori wasu ministoci, bayanai sun fito

"A wannan lokacin ya rantse cewa ba shi da alaƙa da ƴan bindiga, ya kuma yi addu’ar duk wanda ke da hannu kan ayyukan ƴan bindiga a jihar, Allah ya hukunta shi."
"Shi (Matawalle) ƙarya yake yi. Mun ambaci sunaye. Ya fito ya wanke kansa.  Yana buƙatar ya bayyana dangantakarsa da su."
"Waɗannan mutanen biyu, su ne ya bai wa Hilux da kuɗi da kayan abinci domin rabawa ƴan bindiga. Domin haka, wannan ba zargi ba ne, muna da hujjoji kuma NSA na sane da hakan."

- Sulaiman Idris

Gwamna Dauda ya kai ƙarar Matawalle

"Lokacin da gwamna ya gana da shugaban ƙasa, ya kuma bayyana masa duk waɗannan abubuwan. Ya kuma bayyanawa NSA cewa halin da ake ciki kenan kuma waɗannan su ne hujjojin da muke da su."
"Amma tun da yanzu so yake a kawo hujjoji, ina tabbatar muku da cewa za mu fito da gaskiyar lamarin."

Kara karanta wannan

Karkatar da tallafi: Ɗan majalisa ya fusata, ya shirya maka gwamna a gaban kotu

- Sulaiman Idris

Matawalle ya zargi Gwamna Dauda

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi martani kan zargin ɗaukar nauyin ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Matawalle ya musanta zargin da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi masa kan cewa shi ne ke ɗaukar nauyin ƴan bindiga a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng