Matawalle Ya Fadi Yadda Ya Kwaci Dauda Lawal daga Hannun EFCC, Ya Kalubalance Shi

Matawalle Ya Fadi Yadda Ya Kwaci Dauda Lawal daga Hannun EFCC, Ya Kalubalance Shi

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya caccaki Gwamna Dauda Lawal Dare kan sukarsa da yake yi
  • Matawalle ya bayyana yadda ya taimakawa Dauda Lawal da muƙamin hadimi wurin samun fasfo da EFCC ta kwace masa
  • Karamin Ministan tsaro ya ce ko kadan bai damu da abin da Lawal ke fada a kansa ba saboda ya dauke shi kamar hadiminsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT Abuja - Ƙaramin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi magana kan Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.

Bello Matawalle ya fadi yadda ya taimaki Dauda Lawal lokacin da EFCC ke nemansa ruwa a jallo.

Matawalle ya tona irin rufawa Dauda asiri da ya yi
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya caccaki Gwamna Dauda Lawal. Hoto: Dauda Lawal Dare, Bello Matawalle.
Asali: Twitter

Bello Matawalle ya ce ya taimaki Dauda Lawal

Kara karanta wannan

“Bai taba cin zabe a Edo ba;” Mataimakin gwamna ya yi shagube ga gwamnansa

Tsohon gwamnan Zamfara ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Talata 24 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matawalle ya ce ya taimaki Dauda Lawal wurin samar masa da fasfo bayan an kwace na shi a Najeriya.

Karamin Ministan ya ce Dauda Lawal ya roke shi ya ba shi mukamin hadiminsa domin rubuta wasika ga hukumar shige da fice.

"Lokacin da Dauda ke da matsala da EFCC, sun kwace fasfo na shi yadda ba zai iya tafiya ba."
"Ya je wurin hadimina, Bahir Yuguda ya roke shi da ya mani magana a ba shi hadimi na musamman, na ce masa babu damuwa."
"Na kira Dauda na ce masa ba mu da ofis da za mu ba shi, ya ce kawai wasikar ya ke so, daga nan muka ba shi takarda ya kai ta ofishin shige da fice aka ba shi fasfo."

Kara karanta wannan

"Sama da mutum miliyan 88 na fama da talauci," Sheikh Pantami ya ba matasa mafita

- Bello Matawalle

Matawalle ya fadi yadda Dauda ya tsere

Matawalle ya ce daga nan Dauda ya wuce Kebbi zuwa Nijar kafin daga nan ya tsallake zuwa Birtaniya.

Ya ce bayan wata biyu EFCC suka turo wasika cewa suna binciken Dauda amma ya samu fasfo daga gwamantinsa ya gudu.

Zamfara: APC ta roki Tinubu kan ta'addanci

Kun ji cewa Jam'iyyar APC reshen Zamfara ta bukaci Bola Tinubu ya sanya dokar ta baci a jihar saboda matsalar ta'addanci.

Kakakin jam'iyyar, Yusuf Idris shi ya tabbatar da haka inda ya ce akwai masu neman kawo cikas a yaki da ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.