Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta Yi Babban Rashi, Jami'ai 5 Sun Mutu a Hatsarin Mota

Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta Yi Babban Rashi, Jami'ai 5 Sun Mutu a Hatsarin Mota

  • Bayanan da muka samu na nuni da cewa jami'an rundunar 'yan sandan Kano sun rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su
  • An rahoto cewa hatsarin mota ya rutsa da kimanin jami'an 'yan sandan 15 a hanyarsu ta komawa Kano daga aikin zabe a Edo
  • Ya zuwa yanzu dai rundunar 'yan sandan jihar ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba amma ance jami'an na kwance a asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rahotanni sun bayyana cewa jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano sun yi hatsarin mota a hanyarsu ta komawa Kano daga Edo.

An ce hatsarin motar ya rutsa da akalla jami'an 'yan sandan Kano 15 inda biyar suka mutu yayin da sauran 10 suka jikkata.

Kara karanta wannan

Dakaru sun kara yin gagarumar nasara, sojoji sun hallaka abokin Bello Turji

'Yan sandan Kano 5 sun rasu a hatsarin mota.
Allah ya yiwa 'yan sandan Kano 5 rasuwa a hatsarin mota. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Kano: 'Yan sanda sun yi hatsari

Rahoton da gidan rediyon Freedom ya fitar ya nuna cewa 'yan sandan sun yi hatsari ne a hanyarsu ta komawa Kano bayan sa ido a zaben gwamnan Edo da aka kammala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto cewa hatsarin ya faru ne a daren jiya Litinin, 23 ga watan Satumbar 2024 a daidai garin Karfi na karamar hukumar Kura da ke jihar Kano.

An kuma bayyana cewa motar yan sandan ta kamfanin Kano Line ta yi karo da wata babbar motar tirela, lamarin da ya kai ga ajalin jami'ai biyar da jikkata 10.

'Yan sanda 5 sun mutu a Kano

Wata majiya ta lissafa sunayen 'yan sandan da suka rasu da suka hada da Sufeta Usman Salishu, Sajan Umar Muhammad da Kofur Kamalu Shehu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun aika 'yan ta'adda 8 lahira, an ceto wanda aka yi garkuwa da su

Sauran sun hada da Sajan Sa’idu Salisu da Kofur Abubakar Nuhu, kuma an tabbatar da rasuwar ne a asibiti mafi kusa da aka garzaya da su bayan hatsarin.

Hakazalika, an ce 'yan sanda 10 da suka jikkata yanzu haka suna kwance a asibitin kwararru na Murtala inda suke samun kulawar likitoci.

Har kawo yanzu dai ba a ji ta bakin rundunar 'yan sandan jihar Kano kan wannan lamari ba yayin da kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa bai amsa sakon da muka aika masa ba.

Kano: An ceto 'yar shekara 2

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta samu nasarar kubutar da wata yarinya 'yar shekara biyu da aka yi garkuwa da ita.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da ceto yarinyar awanni 16 da sace ta cikin koshin lafiya a makota, bayan da aka nemi N2m kudin fansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.