Yanzu-yanzu: PSC ta kori manyan 'yan sanda 10 daga aiki
Hukumar kula a ayyukan 'yan sanda (PSC), ta kori manyan jami'an 'yan sanda 10 tare da ragewa wasu 8 matsayi saboda wasu laifuka da suka aikata.
Wannan na kunshe ne a wata takarda da shugaban fannin yada labarai da hulda da jama'a na hukumar, Ikechukwu Ani, ya fitar a ranar Litinin.
Ani ya ce an yanke wannan hukuncin a taro karo na 8 da hukumar tayi wanda ya kwashe makonni uku kuma ya kare a ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2020, jaridar The Nation ta wallafa.
Duk da takardar bata bayyana sunayen jami'an da hakan ta shafa ba, ta bayyana cewa akwai dan sanda daya mai mukamin sufirtanda, biyar masu mukamin mataimakin sufirtanda sai wasu hudu masu mukamin ASP.
"Wani mataimakin kwamishinan 'yan sanda da CSP duk an rage masu matsayi, hukuncin ya shafi wani dan sanda mai mukamin SP, daya SSP sai wani ASP.
"Hukumar ta amince da bai wa wasu jami'ai 16 hukunci mai tsauri da kuma wasikar jan kunne ga wasu hudu. Wasu biyu za su karba wasikar shawara yayin da wasu 12 za su karba wasikar dora laifi.
"Hukumar ta duba al'amura 83 na masu laifuka da suka hada da 8 na daukaka kara sai wasu korafe-korafe.
"Hukumar ta amince da karin girman manyan 'yan sanda 6,618 da suka hada da AIG zuwa DIG, kwamishinoni 4 zuwa AIG da kuma DCP uku zuwa CP," takardar tace.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: DSS ta cafke Magu, shugaban EFCC
A wani labari na daban, a samamen da 'yan sandan kasar Kenya su ka kai wani gidan haya da ke jerin rukunin gidajen haya da ke Sango, a birnin Homa Bay a ranar Juma'a, sun kama dalibai 35 na firamare da sakandire.
A yayin da 6 suka tsere, yara mata 20 da maza 15 masu shekaru 13 zuwa 17 sun shiga hannu bayan sun yi mankas da giya kuma tsirara, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
An samu kwaroron roba da aka yi amfani da su a dakunan baccin gidan. Shugaban 'yan sandan yankin, Robert Lango ne ya jagoranci sauran jami'an inda suka damke yaran 'yan makaranta.
Lango ya ce wasu iyaye ne suka karbar wa 'ya'yansu biyu mata hayar gidan, amma sai makwabta suka sanar da hakan bayan jin sauti mai amo. An damke mamallakin gidan mai suna Patrick Ayieko.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng