Sojoji Sun Aika 'Yan Ta'adda 8 Lahira, An Ceto Wanda Aka Yi Garkuwa da Su

Sojoji Sun Aika 'Yan Ta'adda 8 Lahira, An Ceto Wanda Aka Yi Garkuwa da Su

  • Dakarun rundunar sojan kasar nan sun yi nasarar fatattakar yan ta'adda tare da aika takwas daga cikinsu lahira
  • Jami'an tsaro sun samu nasarar ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na kasar nan
  • Rundunar ta bayyana cewa an yi nasarar dakile hari kan mazauna kauyukan jihar Borno tare da cafke makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Dakarun sojan kasar nan sun fatattaki yan ta'adda a sassa daban-daban na kasar nan tare da hallaka takwas daga cikinsu.

A gagarumin aikin da jami'an rundunar sojan suka yi, an yi nasarar ceto wasu mutane 16 da aka yi garkuwa da su ana neman kudin fansa.

Kara karanta wannan

Dakaru sun kara yin gagarumar nasara, sojoji sun hallaka abokin Bello Turji

Sojoji
Sojoji sun hallaka yan ta'adda 8 Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa sojoji sun kuma samu tarin miyagun makamai daga yan ta'addan da su ka sha luguden wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun fatattaki yan ta'adda

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa dakarun sojan kasa sun tarwatsa wasu masu garkuwa da mutane a kauyen Uvaha da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno.

Wannan ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu na cewa yan bindigar na kora wasu mutane da su ka sato da zummar neman kudin fansa da yan uwansu.

Borno: Sojoji sun dakile harin yan ta'adda

Rundunar sojan Najeriya ta bayyana cewa jami'anta sun dakile harin da yan ta'adda su ka shirya kai wa wasu kauyuka da ke jihar Borno.

An gano yan ta'addan sun yi niyyar kai harin ne domin samun kayan amfani, amma sojoji su ka tarwatsa su tare da kashe uku daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Baki har kunne: Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya samu manyan nasarori a cikin mako 1

Sojoji sun damke yan ta'adda

A baya kun ji cewa rundunar sojin kasar nan ta cafke masu garkuwa da mutane a jihar Taraba bayan an samu bayanan sirri kan zarginsu da sace mutane don kudin fansa.

Mukaddashin mataimakin daraktan yada labarai na rundunar, Kyaftin Olubodunde Oni ne ya bayyana cewa dakarun operation Whirl stroke ne su ka damke yan ta'addan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.