Ta Dikko Dakin Kara: Katsina Ta Cika Shekaru 37 da Kafuwa, An Fara Shirin Biki

Ta Dikko Dakin Kara: Katsina Ta Cika Shekaru 37 da Kafuwa, An Fara Shirin Biki

  • A ranar 23 ga watan Satumba, jihar Katsina ta cika shekaru 37 da kafuwa bayan da Janar Ibrahim Babangida ya cire ta daga Kaduna
  • Gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Radda ta bayyana shirye-shiryen da ta ke yi na gudanar da bikin murnar cika shekaru 37
  • Kwamishinan watsa labarai na jihar, Bala Zango ya ce a ranar bikin, Farfesa Isa Ali Pantami zai gabatar da wa'azi a kan rikon amana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Umaru Radda ta bayyana shirye-shiryenta na bikin cika shekaru 37 da kafa jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Dakta Bala Zango, ya bayyana shirin gwamnatin kan bikin murnar ranar a wani taron manema labarai.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishina a Kaduna ya zama shugaban PDP, ya shirya ɗaiɗaita APC

Gwamnatin Katsina ta fara bikin cikar jihar shekaru 37 da kafuwa
Murnar cika shekaru 37: Gwamnatin Katsina ta fara shirye-shiryen shagalin biki. Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Kwamishinan ya ce bikin zai tuna da irin jagorancin Janar Ibrahim Babangida mai hangen nesa, wanda ya kafa jihar Katsina a ranar 23 ga Satumba, 1987, inji rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kadan daga tarihin jihar Katsina

Jihar Katsina ta na iyaka da Jamhuriyar Nijar daga Arewa sai jihar Kano daga gabas, Kaduna ta bangaren Kudu da kuma Zamfara daga bangaren Yamma.

Ana yi wa Katsina lakabi da "ta Dikko dakin kara" yayin da babban birnintada kuma garin Daura sun kasance "wurare na al'adu, addini da kuma tarihi" inji WikiPedia.

An kafa Katsina a shekarar 1987 kuma an ciro ta ne daga Kaduna. Jihar Katsina ce ta biyar a mafi yawan al'umma a kasar nan da sama da mutane 5,800,000 bisa kididdigar 2006.

A ‘yan shekarun nan, jihar Katsina na daya daga cikin jihohin Nijeriya da ‘yan bindiga, masu garkuwa da barayin shanu suka fi addabarsu.

Kara karanta wannan

Yunwa na neman kashe shi a Katsina, Kwankwaso ya ceci ran karamin yaro

Gwamnatin Katsina ta fara shirin biki

Kwamishinan watsa labaran jihar ya ce gwamnati ta shirya hada kan 'yan jihar domin murnar nasarorin da aka samu da kuma duba abubuwan da za a cimmawa a nan gaba.

Daily Nigerian ta ruwaito gwamnatin Radda ta kaddamar da wani babban kwamitin bisa jagorancin sakataren gwamnati, Abdullahi Garba Faskari domin shirya bikin.

Kadan daga cikin shirye shiryen akwai taron ba da kyaututtuka da kuma wa'azi daga fitaccen malamin addini, Farfesa Isa Ali Pantami mai taken 'Rikon Amana.'

Gwamnan Katsina ya yi nadin mukamai

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Katsina, Dikko Radda ya nada a naɗa sabbin shugabannin wasu hukumomin gwamnati a jihar guda tara.

Daga cikin wadanda aka hada akwai Alhaji Kabir Usman Amoga, matsayin daraktan hukumar tsaftace mahalli da Hajia Binta Dangani, shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.