Yadda aka gudanar da bikin cikar jihar Katsina shekaru 30 da kafuwa

Yadda aka gudanar da bikin cikar jihar Katsina shekaru 30 da kafuwa

A ranar 23 ga watan Satumba ne jihar Katsina ta cika shekaru 30 da kafuwa, inda aka kirkireta a ranar 23 ga watan satumbar shekarar 1987 tare da jihar Akwa Ibom, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

A ranar asabar din ne aka gudanar da bikin jihar shekaru 30, inda aka gudanar da taruka daban daban ciki har da wasan Polo inda gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel ya samu halarta.

KU KARANTA: Cikin fasinjoji ya ɗuri ruwa yayin da jirgin ƙasa ya mutu a kwanar da ake satar mutane

A zamanin mulkin shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ne aka kirkiri jihohin biyu, inda Manjo janar Abdullahi Sarki Mukhtar ya fara shugabanta a shekarar 1897-1988.

Yadda aka gudanar da bikin cikar jihar Katsina shekaru 30 da kafuwa
Masari

Cikin wadanda aka karrama sun hada da shugaban kasa Ibrahim Babangida, a matsayin wanda ya kirkiri jihar. Haka zalika an karrama wadanda suka yi kokari wajen samar da jihar da suka hada da tsohon minista Wada Nas, Alhaji Sani Zangon Daura da Sarki Mukhtar.

Yadda aka gudanar da bikin cikar jihar Katsina shekaru 30 da kafuwa
Gwamnoni

An karrama gwamnan farar hula na farko a jihar, Alhaji Saidu Barda, tare da tsohon sufeton Yansanda, marigayi MD Yusuf, tsohon Alkalin Alkalai Mohammed Bello, Mai shari’a Mamman Nasir mai ritaya.

Yadda aka gudanar da bikin cikar jihar Katsina shekaru 30 da kafuwa
Taron

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu, gwamnan Jigawa Badaru Abubakar da gwamna Abubakar Tambuwal.

Yadda aka gudanar da bikin cikar jihar Katsina shekaru 30 da kafuwa
Taron

Yadda aka gudanar da bikin cikar jihar Katsina shekaru 30 da kafuwa
Taron

Yadda aka gudanar da bikin cikar jihar Katsina shekaru 30 da kafuwa
Taron

Yadda aka gudanar da bikin cikar jihar Katsina shekaru 30 da kafuwa
Taron

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng