Cika shekaru 32 da kafuwa: Karanta wasu muhimman bayanai game da Katsina

Cika shekaru 32 da kafuwa: Karanta wasu muhimman bayanai game da Katsina

A ranar 23 ga watan Satumba na shekarar 1987 ne gwamnatin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta kirkiro jahar Katsina daga cikin jahar Kaduna, wanda hakan yasa a yau Katsina ta cika shekaru 32 da kirkira.

Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman bayanai daya kamata ku sani game da jahar Katsina, kamar haka;

KU KARANTA: Allah raya jahar Katsina: Gwamnoni 10 da suka mulki jahar Katsina tun 1987

- Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kirkiri jahar Katsina daga Kaduna

- A ranar 23 ga watan Satumbar shekarar 1987 aka kafa jahar Katsina

- Sa’ar jahar Katsina a Najeriya ita ce jahar Akwa Ibom da aka kirkiresu tare

- Katsina ta yi gwamnoni 10 a cikin shekaru 32

- Gwamnan Katsina na farko shi ne Janar Abdullahi Sarki Mukhtar

- Gwamnan farar hula na farko a Katsina shi ne Alhaji Sai’du Barda

- Girman kasar Katsina ya kai murabba’I 24,192, it ace jaha ta 17 wajen girma a Najeriya

- Katsina ce jaha ta 4 wajen yawan Jama’a a Najeriya da jama’a miliyan 5,801,584 a lissafin kidayar shekarar 2006

- Katsina ce jaha ta biyu a Najeriya da ta taba samar da shugaban kasa a Najeriya sau biyu, Buhari da Yar’adua

- Katsina na da kananan hukumomi 34

- Katsina na da jami’o’i guda 3

- Katsina nada Sanatoci 3, da yan majalisun wakilai 15 da yan majalisun jaha guda 34

- Katsina ta iyaka da jahohi 4, Jigawa, Kano, Zamfara da Kaduna

- Jahar Katsina na da manyan masarautu guda 2, Daura da Katsina

A wani labari kuma, jama'an yankin Daura sun bayyana cewa lokaci yayi da ya kamata masu ruwa da tsaki a siyasar jahar Katsina su basu dama su fidda gwamnan jahar Katsina a zaben 2023 sakamakon sauran shiyyoyin biyu sun taba yin gwamna, amma su basu taba yi ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel