Bayan Shafe Watanni 7 a Hannun Yan Bindiga, Yan Jami'ar Gusau Sun Samu Yanci

Bayan Shafe Watanni 7 a Hannun Yan Bindiga, Yan Jami'ar Gusau Sun Samu Yanci

  • Dalibai da malaman da yan bindiga su ka sace a jami'ar FUG da ke Zamfara sun samu nasarar sake ganawa da iyalansu a yanzu
  • Rahotanni sun bayyana cewa dukkanin wadanda aka sace sun samu kubuta daga hannun yan bindigar da su ka yi garkuwa da su
  • Amma ba a tabbatar da hanyar da aka bi wajen kubutar da wadanda aka sace din ba, tun da har yanzu hukuma ba ta ce komai ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Dalibai da malaman jami'ar tarayya ta Gusau (FUG) sun shaki iskar yanci bayan shafe akalla watanni bakwai a hannun yan bindiga.

A watan Satumba, 2023 ne yan bindigiar su ka kai mummunan hari jami'ar tare da sace wasu daga cikin malamai da daliban makarantar.

Dalibai
Dalibai, malaman FUG sun kubuta daga hannun yan bindiga Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Zagazola Makama, masanin tsaro a kasar nan ya wallafa a shafinsa na X cewa ya bayyana cewa dukkanin wadanda aka kwashe a wancan harin sun dawo gida.

Yadda aka sace yan jami'ar Gusau

Jaridar Punch ta wallafa cewa wani Abubakar Sani, mazaunin kauyen Sabon Gida a Zamfara ya bayyana cewa yan bindiga sun kutsa wurin kwanan dalibai a jami'ar FUG.

Ya kara da cewa an shiga wuraren kwanan dalibai har guda uku da 4.00n.s, inda su ka kwashi wadanda tsautsayi ya rutsa da su zuwa daji.

Mutanen Gusau sun shaki iskar yanci

Rahotanni sun tabbatar da cewa dukkanin malaman jami'ar tarayya ta Gusau da sauran wadanda aka kwashe watanni bakwai da su ka wuce sun samu yanci.

Amma ba a tabbatar da yadda aka ceto daliban da malamansu ba, ko an biya yan bindiga kudin fansa ko kuma iya kokarin jami'an tsaro ne ya kubuto da su.

Gwamna ya yi tir da sace daliban jami'ar Gusau

A baya mun wallafa cewa gwamnan jihar Zamfara, ya bayyana takaicin yadda yan bindiga su ka kutsa wurin kwanan daliban jami'an tarayya ta Gusau, tare da sace dalibai da malamansu da dama.

Bayan ya yi Allah wadai da sace dalibai sama da 24, gwamnan Dauda Lawal ya umarci jami'an tsaro su tabbatar da cewa sun ceto dukkanin daliban da malamansu da aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.