TCN: Ƴan Ta'adda Sun Jefa Bam a Hasumiyar Wuta, Mazauna Yobe Sun Shiga Duhu

TCN: Ƴan Ta'adda Sun Jefa Bam a Hasumiyar Wuta, Mazauna Yobe Sun Shiga Duhu

  • Yan ta'adda sun sake kai farmaki kan layin samar da wutar lantarki da ya taso daga Gombe-Maiduguri-Damaturu
  • Wannan ne karo da uku da yan ta'adda ke lalata hanyar samar da wuta a yankin a cikin yan watanni ba kakkautawa
  • Kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ta bakin kakakinsa,ya fadi matakan da aka dauka na samar da wuta na wucin gadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe - Yan ta'adda sun jefa mazauna Damaturu da kewaye cikin duhu bayan sun lalata layin da ke samar masu wutar lantarki da ya taso daga Damaturu-Maiduguri.

An zargi yan ta'adda da lalata layin a ranar Asabar bayan sun jefa bam cikinsa, kamar yadda kamfanin wutar lantarki ta kasa (TCN) ya bayyana.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Yadda APC ta lashe zabe bayan samun nasara a kananan hukumomi 11

Jihar
Yan ta'adda sun lalata hasumiyar TCN a Yobe Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an lalata hasumiyar samar da wutar mai lamba T372 da ke da karfin 330kV, kuma ya taso daga Gombe-Maiduguri-Damaturu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An lalata hasumiyar TCN karo na 3

Arise News ta wallafa cewa wannan ne karo na uku a cikin yan watanni da yan ta'adda ke lalata hasumiyar TCN da ke kai wuta yankin a cikin yan watanni.

Tun bayan aika-aikar da yan ta'addan su ka tafka a ranar Asabar, mutanen Damaturu har zuwa Maiduguri su ka fada cikin duhu.

Yadda yan ta'adda su ka lalata hasumiyar TCN

Manajan hulda da jama'a na TCN, Ndidi Mbah ya bayyana cewa yan ta'adda sun yanke dukkanin kafafu hudu da ke rike da hasumiyar.

Ya kara da cewa za a ba Maiduguri wuta daga tashar wutar lantarki da ke birnin, sannan za a ba Damaturu wuta daga tashar wuta da ke Potiskum.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: ‘Wakilan APC da PDP na ba masu kada kuri'a cin hancin N10000’

TCN na shirin gyara wutar lantarki

A baya mun ruwaito cewa kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya bayyana cewa an samu nasarar gyara wutar da ta rika lalacewa karo na biyu a cikin 2024.

Gyaran ya biyo bayan rugujewar tushen wutan kasar da asali ake kula da shi a tsakiyar birnin Osogbo na jihar Osun, wanda ya jefa jama'a, musamman masu sana'ar kayan sanyi cikin matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.