APC Ta Roki Tinubu kan Ta’addanci a Zamfara, Ta Zargi Gwamna Dauda Lawal
- Jam'iyyar APC reshen Zamfara ta bukaci Bola Tinubu ya sanya dokar ta baci a jihar saboda matsalar ta'addanci
- Kakakin jam'iyyar, Yusuf Idris shi ya tabbatar da haka inda ya ce akwai masu neman kawo cikas a yaki da ta'addanci
- Yusuf ya zargi Gwamna Dauda Lawal karara da cewa bai son yaga an samu nasara a harkar saboda Bello Matawalle
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta roki Bola Tinubu alfarma game da ta'addanci a jihar Zamfara.
Jam'iyyar ta bukaci Tinubu ya sanya dokar ta baci domin kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar.
APC ta zargi Dauda Lawal kan ta'addanci
Kakakin jam'iyyar a jihar, Yusuf Idris shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da Channels TV ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yusuf Idris ya zargi Gwamna Dauda Lawal ta kawo cikas a kokarin yaki da ta'addanci da ake yi a jihar.
Yusuf ya ce gwamnan yana yin haka saboda kiyayyar da ke tsakaninsa da karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.
Ya ce gwamnan yana iya bakin kokarinsa domin ganin ba a samu nasara a yaki da ta'addanci ba saboda siyasa kawai, cewar rahoton Punch.
Yadda ake samun nasara a yaki da ta'addanci
"Wannan yaki da ta'addanci da ake yi a Zamfara karkashin jagorancin Bello Matawalle tabbas ana samun nasara."
"Sai dai abin takaici, Gwamnan Dauda Lawal yana kokarin kawo cikas a nasarorin da ake samu saboda siyasa."
"Yana son yin amfani da rashin tsaro domin siyasarsa ta 2027 kamar yadda a yi a 2023 saboda nasarar yaki da ta'addanci zai iya kawo masa masa cikas."
- Yusuf Idris
An zargi Dauda Lawal da tsanar Matawalle
Kun ji cewa wata kungiyar matasan jam'iyyar APC soki Gwamna Dauda Lawal game da ta'addanci a jihar Zamfara.
Kungiyar ta ce tsanar da Dauda Lawal ya yi wa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ta yi yawa.
Hakan na zuwa ne bayan zargin hannu a ta'addanci da ake yi wa Matawalle a yankin Arewa maso Yamma.
Asali: Legit.ng