Rundunar Tsaro Ta Fadi Halin da Turji Ke ciki bayan Kisan Sabubu, Ta Sha Alwashi
- Yayin da aka hallaka dan ta'adda, Halilu Sabubu, rundumar tsaro ta sha alwashin kawo karshen sauran yan bindiga
- Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce za su kawo karshen rikakken dan ta'adda, Bello Turji nan ba da jimawa ba
- Janar Musa ya kuma gargadi al'umma da ke taimakon yan bindiga ta bangarori da dama da su yi hankali da hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya sha alwashin game da kawo karshen Bello Turji.
Janar Musa ya ce suna kokarin ganin sun samu nasara kan dan ta'addan duba da halin da ya ke ciki yanzu.
Rundunar tsaro za ta gama da Turji
Hafsan tsaron ya fadi haka a cikin wani bidiyo yayin hira da Arise TV da shafin Zagazola Makama ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Janar Musa ya ce yana da tabbacin kawo karshen dukan rikakkun yan bindiga da ke addabar al'umma.
Ya roki yan Najeriya wurin ba su hadin kai inda ya ce akwai masu taimakonsu da abubuwa da dama.
"Lokacin da na ce za mu kawo karshensu, washe-gari mun yi nasarar hallaka Sabubu, abin da zai faru kenan da Turji."
"Ina ba ku tabbacin cewa Turji a birkice ya ke, ya tsere kuma ya sani hatta yan bindiga yan uwansa nemansa suke yi saboda halin da ya saka su."
"Za mu cigaba da kai musu farmaki har sai mun ga mun samu nasara kansu duk da taimaka musu da wasu miyagu daga cikin al'umma ke yi."
- Janar Christopher Musa
Janar Musa ya shawarci al'umma
Janar Musa ya shawarci gwamnoni su dakatar da amfani da manyan babura wanda da su suke amfani wurin kai hare-hare da harkokinsu.
Ya gargadi wasu mutane da ke taimakon yan bindiga da su guji ranar da za su cafke su saboda kamar yan bindiga suke su ma.
Bidiyon Sabubu na karshe a duniya
Kun ji cewa an wallafa faifan bidiyo inda marigayi dan ta'adda, Halilu Sabubu ya ke rokon yan uwansa kan lamarin tsaro.
Sabubu ya kira manyan yan bindiga da suka hada da Bello Turji da Alhaji Ado da Alhaji Shingi domin shawo karshen lamarin.
Asali: Legit.ng