Ambaliyar Ruwa: Buhari Ya Tura Pantami Ya Wakilce Shi Wajen Jajantawa 'Yan Maiduguri
- Isa Ali Ibrahim Pantami ya wakilci Muhammadu Buhari domin yi wa mutanen Borno ta’aziyyar ambaliyar ruwa
- Malamin da ya rike ministan sadarwa a gwamnatin bayan ya jagoranci tsofaffin ministocin da suka yi aiki a 2019-23
- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce Buhari ya aiko da kyautar kudi amma ba a bayyana gudumuwar nawa ya ba da
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Borno - An samu mummunar ambaliyar ruwan da ta shafi miliyoyin mutane a kananan hukumomin Maiduguri da Jere a jihar Borno.
Mutane da yawa sun ziyarci garin Maiduguri domin jajanta masu, Muhammadu Buhari yana cikin wadanda aka sa ran gani, bai je ba.
Farfesa Isa Pantami ya wakilci Buhari a Borno
A ranar Asabar, Isa Ali Ibrahim Pantami ya sanar a shafinsa na X cewa ya wakilci tsohon shugaban kasar wajen ziyarar ta’aziyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce ya wakilci Muhammadu Buhari GCFR domin jajantawa gwamnati da mutanen jihar Borno.
Pantami ya isar da sakon Buhari
Tsohon ministan sadarwan da tattalin arzikin zamanin ya gana da Mai girma Babagana Umar Zulum OON da Mai martaba Shehun Borno.
Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar Maiduguri da Jere su ka jajircewa tare da yin addu’a Allah SWT ya ji kan wadanda aka rasa.
Ya yi addu’a ga Ubangiji Sarki ya yafewa wadanda aka rasa, Ya warkar da marasa lafiya kuma Ya maida arzikin wadanda suka yi rashi.
A sanarwar da aka fitar, an ji Muhammadu Buhari ya yi magana da mutanen ta tarho kuma ya ba da kyautar da a bayyana adadinta ba.
Buhari ya ba mutanen Maiduguri kudi
A cikin tawagar ta shi akwai Hon. Chukwuemeka Nwajiuba wanda ya rike matsayin karamar ministan ilmi a gwamnatin na Buhari.
Nwajiuba ya gabatar da kyautar kudin da Buhari ya gabatar a madadin wadanda suka yi aiki da tsohon shugaban kasar a 2019-2023.
Shi kuwa Isa Pantami wanda malamin musulunci ne ya yi addu’a ta musamman domin cigaba da zaman lafiya a jihar da kasar nan.
Tallafin ambaliyar garin Maiduguri
Rahoto ya zo cewa Aliko Dangote ya ba da rabin abin da gwamnatin tarayya ta aika jihar Borno, Aminu Dantata ma ya ba da N1.5bn.
Gwamnonin jihohi da ‘yan majalisar tarayya, attajirai sun aiko da gudumuwa kuma ana sa ran wasu za su cigaba da makudin kudi.
Asali: Legit.ng