Tsohon Shugaban NESG Ya FadI Kuskuren Tinubu da Ya Jefa Ƴan Najeriya cikin Wahala

Tsohon Shugaban NESG Ya FadI Kuskuren Tinubu da Ya Jefa Ƴan Najeriya cikin Wahala

  • Tsohon shugaban NESG ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya biyo hanya mai gargada wajen cire tallafin man fetur a Najeriya
  • Kyari Bukar ya ce kamata ya yi shugaban ƙasa ya rika cire 5% na tallafin mai duk bayan watanni shida don kaucewa halin da ƴan Najeriya za su shiga
  • A cewsrsa, yana da kyau a tuge tallafin amma ya kamata a kalli ƙunci da wahalar da mutane za su shiga tun farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon shugaban wata ƙungiyar rattalin arziki (NESG), Kyari Bukar, ya ce kamata ya yi shugaba Bola Tinubu ya bi a hankali a hankali ya cire tallafin man fetur.

Kyari Bukar ya bayyana cewa bi hankali wajen cire tallafin mai zai taimaka wajen magance wahalar da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a ciki.

Kara karanta wannan

"In Sha Allahu za mu ɗinke ɓaraka," Gwamna ya gano waɗanda suka haddasa rikici a PDP

Shugaba Tinubu.
Kyari Bukar ya gano kuskuren da aka yi wajen cire tallafin mai a Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Tsohon shugaban NESG ya tausaya wa mutane

A cewarsa, da a ce shugaban ya riƙa cire kaso 5% na tallafin mai duk bayan watanni shida, ƴan Najeriya ba za su ji zafin cirewar farat ɗaya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukar ya bayyana hakan ne a cikin wani shiri da gidan talabijin na Channels tv ke haskawa ranar Jumu'a.

Kyari Bukar ya ce:

"Idan kana son kawo tsarin tattalin arziki, to ra'ayoyin waɗanda wannan tattalin arzikin ya shafa yana da muhimmanci.
"Idan kuma ka zo da wata manufa da za ta kawo cikas da illa ga tattalin arziki, za su juya maka baya ne ko kuma su nemo hanyoyin da za su murƙushe manufar.

Kuskuren Tinubu a cire tallafin mai

Tsohon shugaban NESG ya ce mutane sun fusata a ƙasar nan kuma idan aka duba yanayin tattalin arziki, tabbas ƴan ƙasa na fama da yunwa.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaba a APC ya caccaki Tinubu, ya fadi yadda Abacha ya yi masa fintinkau

Kyari Bukar ya ce duk halin da al'umma suka shiga yanzu ya samo asali ne daga illar tuge tallafin man fetur da kuma yunkurin daidai canjin Naira.

A rahoton The Cable, Bukar ya ce:

"Dukkansu manufofi ne ma su kyau idan da an bi hanyar da ta dace, ni a ganina da an bi a hankali a hankali wajen cire tallafin man fetur.
"Mun gano illolin da ka iya biyo baya waɗanda ba a yi tsammani ba kuma an sanar da shugaban ƙasa tun kafin ya hau mimbari ya sanar. Manufar tana da kyau amma hanyar da aka bi tana da illa."

NNPCL ya yi magana kan matatun gwamnati

A wani rahoton kuma kamfanin man Najeriya na NNPCL ya yi bayani kan korafin da yan kasa ke yi game da matatun man gwamnati musamman na Fatakwal

NNPCL ya ce ba gazawa ba ce ko rashin shiri ya saka matatar man Fatakwal gaza fara aiki sai dai kawai akwai shirye shiryen da suke yi ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262