CBN Yana Harin Naira Biliyan 50 daga Harajin da Za a Matso hannun ‘Yan Najeriya
- An dage sai an kakaba haraji a kan duk kudin da mutane su ke turawa ta kafofin zamani da yanar gizo a Najeriya
- Bankin CBN ya sake dawo da harajin tsaron yanar gizo wanda ake lissafin zai kawowa Najeriya kimanin N50bn
- A shekarar 2024, gwamnatin tarayya za ta iya tatsar N50bn daga harajin domin za a aika kusan N999tr ta yanar gizo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Babban bankin Najeriya watau CBN ya ci burin samun kusan Naira biliyan 50 nan da karshen shekarar nan ta 2024.
Babban bankin na CBN zai samu wadannan kudin shiga ne a dalilin harajin tsaron yanar gizo da aka sake dawo da shi a yanzu.
Haraji zai tatsowa CBN N50bn
Masana tattalin arzikin su ka bayyana cewa za a iya samun N50bn daga wannan haraji da za a rika karba a cewar jaridar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban sashen bincike na kamfanin FMDQ, Vincent Nwani, ya ce ana tsammanin CBN ya iya samun N50bn daga harajin tsaron.
Vincent Nwani ya dogara ne da cewa a shekarun 2022 da 2023, an yi hada-hadar kudin da sun kai N987tr ta kafofin yanar gizo.
Rahoton ya ce an samu wadannan bayanai ne daga alkaluman na’urar NIBSS da ke kula da hada-hadar kudi a bankunan Najeriya.
CBN za ta karbi 0.005% na kudin hada-hada
Idan aka dauki 0.005% na wannan kudi da CBN yake so ya rika karba a matsayin haraji, gwamnatin Najeriya za ta samu N49.35bn.
Premium Times ta ce a duk kudin da aka aika ta yanar gizo, bankin CBN zai rika daukar wani kaso da sunan ba da tsaro da kariya.
Masanin ya ce a shekarar 2022, an aika N378tr ta yanar gizo wanda hakan ya ba da dama gwamnati ta samu harajin kusan N20bn.
Za a aika N990tr ta yanar gizo
A shekarar 2023 kuwa da aka ga tasirin canjin manyan Nairori, an aka aika N600tr ta kafofin zamanin, sai da harajin ya kai N30bn.
Nwani yana ganin a shekarar nan, za a aika N999tr ta bankuna ta hanyoyin POS da sauran kafofin zamani na aika kudi zuwa bankuna.
An taso gwamnonin CBN a gaba
Bayanai sun nuna ana tuhumar CBN da batar da biliyoyin kudi domin sayen motoci da sunan kama hayan gidajen haya a Najeriya.
Wani rahoton ya ce an yi sama da kusan N10bn domin motocin gwamnoni kuma akwai zargin CBN ya kashe N1bn a gidajen haya.
Asali: Legit.ng