"Akwai Kulli a Ransa": An Zargi Gwamna da Kawowa Matawalle Cikas a Yaki da Ta'addanci
- Wata kungiyar matasan jam'iyyar APC soki Gwamna Dauda Lawal game da ta'addanci a jihar Zamfara
- Kungiyar ta ce tsanar da Dauda Lawal ya yi wa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ta yi yawa
- Hakan na zuwa ne bayan zargin hannu a ta'addanci da ake yi wa Matawalle a yankin Arewa maso Yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Matasan jam'iyyar APC sun caccaki Gwamna Dauda Lawal kan ta'addanci a jihar.
Kungiyar Youth Wing Mobilisation Vanguard ta zargi Dauda Lawal da neman rusa kokarin karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.
Ta'addanci: An soki gwamna kan Matawalle
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Alhaji Ashiru Tukur-Sadauki ya fitar, cewar rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Ashiru ya ce abin takaici ne yadda Dauda Lawal ya tsani Bello Matawalle da kuma Gwamnatin Tarayya, Vanguard ta ruwaito.
Ya ce halayen Dauda Lawal game da tsanar da ya ke yi wa Tinubu da Matawalle na kawo cikas a yaki da ta'addanci.
An zargi gwamna da kawo cikas a ta'addanci
"Niyyarsa ita ce kashewa sojoji karfin guiwa a yaki da suke yi da ta'addanci da nasarorin da suke samu."
"Babu dalilin da zai saka Dauda Lawal barin aikinsa na shugaban tsaron jihar, ya kamata a samu hadin kai da shi domin kare rayukan al'umma."
"Sai dai gwamnan ya mayar da hankali wurin bata sunan Bello Matawalle ta kowace hanya."
Wannan na zuwa ne bayan zarge-zargen da ake yi wa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle da cewa yana da hannu a harkar ta'addanci da ake yi musamman a Arewa maso Yamma.
- Alhaji Ashiru Tukur-Sadauki
"Mahaifin Turji mutumin kirki ne" - Sheikh Asada
Mun ba ku labarin cewa Malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada ya fadi halayen mahaifin Bello Turji.
Sheikh Asada ya ce mahaifin kasurgumin dan ta'addan mai suna Usman Mani ya kasance mutumin kirki ne.
Malamin ya ce bakin cikin Turji ya tilasta Mani komawa Kano kafin ya sake tafiya jihar Jigawa domin rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng