'Ya So Biya Mana Kudin Jirgi,’ Yan Kwadago Sun Tono Sirrin Zamansu da Tinubu

'Ya So Biya Mana Kudin Jirgi,’ Yan Kwadago Sun Tono Sirrin Zamansu da Tinubu

  • Kungiyar kwadago ta cigaba da bayani ga yan Najeriya kan abubuwan da suka tattauna da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Shugaban yan kwadago, Joe Ajaero ya ce wata rana Bola Tinubu ya so biya musu kudin jirgi domin zuwa kasashe a kan kudin fetur
  • Kwamared Ajaero ya yi bayanin ne kan yadda suka tattauna game da karin kudin fetur da mafi ƙarancin albashin ma'aikata a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Ƙungiyar kwadago ta jaddada cewa ta yarda da N70,000 a mafi ƙarancin albashi ne saboda kar a kara kudin fetur.

Joe Ajaero ya ce akwai abubuwa da suka faru a lokacin tattaunawa da Bola Tinubu kan karin albashi.

Kara karanta wannan

Kuɗin fetur: Yan kwadago sun raina sabon albashin N70,000, za su sake bugawa da Tinubu

Yan kwadago
Yan kwadago sun fadi yadda suka tattauna da Tinubu. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Joe Ajaero ya ce Bola Tinubu ya so ya biya musu kudin jirgi domin zuwa wasu ƙasashe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya so biyawa 'yan kwadago kudin jirgi

Joe Ajaero ya ce akwai ranar da suke tattauanawa a kan karin albashi zuwa N250,000 da kara kudin fetur.

A lokacin ne shugaban kasa Bola Tinubu ta ce zai ba yan kwadago kudin jirgi su je kasashe su ga yadda ake sayar da man fetur da tsada.

Shugaban kwadago ya ce sun ki karbar kudin ne saboda yan Najeriya ba za su fahimci abin da ya faru ba, wasu za su ce an ba su cin hanci be.

Kungiyar NLC ta ce Tinubu ya yaudare ta

Kungiyar NLC ta ce duk wannan tattaunawa da suka yi da Bola Tinubu amma sai ga gwamnati ta ce ba ta san da haka ba sam.

Kara karanta wannan

An yi watsi da albashin N70,000, an bukaci NLC ta tursasawa Tinubu biyan N250,000

New Telegraph ta ce Joe Ajaero ya yi zargin cewa saboda haka ne ma gwamnatin ta kirkiro zargin ta'addanci domin kawar da hankalinsu har aka kara kudin mai.

Kungiyar kwadago ta ce ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta nemo mafita ga yan Najeriya kan tsadar man fetur tun kafin lamura su rincaɓe.

NLC za ta sake zama da Tinubu

A wani rahoton, mun ji cewa kungiyar kwadago ta nuna bacin rai kan karin kudin fetur da gwamnatin tarayya ta yi bayan sun samu yarda kan ƙarin albashi.

Shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce N70,000 ba za ta tsinana komai ga ma'aikatan Najeriya ba lura da yadda aka kara kudin fetur a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng