Kuɗin Fetur: Yan Kwadago Sun Raina Sabon Albashin N70,000, Za Su Sake Bugawa da Tinubu
- Kungiyar kwadago ta nuna bacin rai kan karin kudin fetur da gwamnatin tarayya ta yi bayan sun samu yarda kan ƙarin albashi
- Shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce N70,000 ba za ta tsinana komai ga ma'aikatan Najeriya ba lura da yadda aka kara kudin fetur
- Haka zalika Kwamared Ajaero ya bayyana cewa za su sake zama da gwamnatin tarayya kan samar da mafita ga talakawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Ƙungiyar yan kwadago ta sake nuna damuwa kan karin kudin fetur da aka samu a Najeriya.
Shugaban yan kwadago, Kwamared Joe Ajaero ya ce dole a sake zama da gwamnatin tarayya kan samar da mafita ga ma'aikatan Najeriya.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Joe Ajaero ya yi bayani ne yayin wani taro kan kaddamar da mafi ƙarancin albashi a jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan kwadago sun yi watsi da N70,000
Shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero ya ce mafi ƙarancin albashin N70,000 ba zai tsinana komai ba a halin yanzu.
Jaridar New Telegraph ta ce Joe Ajaero ya bayyana cewa fa'idar ƙarin albashi zuwa N70,000 ta rushe tun kafin a fara biyan kudin.
Dalilin NLC na watsi da albashin N70,000
Kungiyar kwadago ta bayyana cewa karin kudin man fetur ne ya sanya su nuna damuwa kan N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Joe Ajaero ya ce karin kudin fetur ya jawo kudin ba zai yi amfani ga talaka ba ko da an ba shi su a halin da ake ciki.
'Yan kwadago za su zauna da Tinubu
Kwamared Joe Ajaero ya ce za su nemi zama da gwamnatin tarayya kan ƙarin kudin fetur da tsadar rayuwa da ake fuskanta.
Joe Ajaero ya ce za su zauna da Bola Tinubu a kan ya samar da mafita ga yan Najeriya kan karin kudin fetur da ya yi.
NUP ta yi watsi da albashin N70,000
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar yan fansho a Kudancin Najeriya ta yi watsi da maganar ƙarin albashi zuwa N70,000 da gwamnatin tarayya ta yi.
Kungiyar ta ce mafi ƙarancin albashin ba zai tabuka komai ba lura da yadda ake tsadar rayuwa da kuma karin kudin man fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng