Lissafin Gwauraye Ya Cabe, Sadakin Aure Ya Kara Tsada yayin da Naira Ta Karye

Lissafin Gwauraye Ya Cabe, Sadakin Aure Ya Kara Tsada yayin da Naira Ta Karye

  • Kwamitin ganin wata na kasa ya sanar da cewa sadakin aure ya koma N141,932 wanda kuma daidai yake da haddin yin sata
  • A bangaren fitar da Zakkah kuwa, kwamitin ya ce nisabin Zakkah yanzu ya koma N11,354,560 yayin da diyyar rai ta kai N567,728,000
  • A zantawarmu da wani malamin addini, Goni Abubakar Sa'id ya ce ba laifi idan waliyyan miji da mata suka daidaita a kan kudin sadaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kwamitin ganin wata na kasa karkashin majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya ta fitar da sabon farashin sadaki, diyyar rai da haddin sata.

Kwamitin ya fitar da jadawalin kudaden a ranar 17 ga watan Rabi’ul Awwal, 1446 (Hijira) wanda ya yi daidai da 20 ga watan Satumbar 2024 (Girigoriya).

Kara karanta wannan

CBN yana harin Naira Biliyan 50 daga harajin da za a matso hannun ‘yan Najeriya

Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta fitar da sabon jadawalin sadaki, diyyar rai, haddi da nisabin Zakkah
Sadakin aure ya kara tsada zuwa N141,932 yayin da nisabin Zakkah ya koma N11.3m. Hoto: mc_raheena/Instagram, Egar Anugrah/Getty Images
Asali: Getty Images

Sadakin aure ya kara tsada a Najeriya

A halin yanzu, sadakin aure ya tashi zuwa N141,932 wanda kuma daidai yake da kudin haddin sata kamar yadda kwamitin ya sanar a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda bayani ya nuna, sadaki shi ne mafi ƙarancin adadin da mutum zai iya biya a matsayin kudin auren mace da shari'a ta kayyade.

Hakazalika, sadakin ya yi daidai da kudin da mutum zai sata kafin a yanke masa haddin sata, watau a yanke masa hannu bisa shari'ar Musulunci.

Diyyar rai a Najeriya ta kai N567.7m

Kudin diyya ko kudin jini, shi ne adadin da za a biya a matsayin diyya na kashe musulmi bisa kuskure. A Musulunci, ana biyan kudin diyya ne ga magadan wanda aka kashe.

Kwamitin duba ganin watan ya sanar da cewa diyyar rai a yanzu ta tashi zuwa N567,728,000 kamar yadda shari'a ta tanadar.

Kara karanta wannan

Kuɗin fetur: Yan kwadago sun raina sabon albashin N70,000, za su sake bugawa da Tinubu

Nisabin Zakkah ya koma N11.3m

Zakkah na daya daga cikin shika-shikan Musulunci kuma Annabi Muhammad (S.A.W) ya kasance yana mai nusar da Musulmi muhimmancin fitar da Zakkah.

A halin yanzu, mutum zai fitar da Zakkah ne idan jimillar dukiyarsa ta kai darajar N11,354,560, kuma ana fitar da ita idan dukiya ta shekara a hannu.

Dole a biya sadakin da shari'a ta yanke?

A zantawarmu da Goni Abubakar Sa'id, limamin babban masallacin Juma'a na Zaria Road da ke Funtua, ya ce ba dole sai abin da kwamitin ya yanke ne za a biya matsayin sadaki ba.

Goni Abubakar ya ce kiyasin da kwamitin ya yi yana kan mazhabar Malikiya kuma ana so ayi biyayya a kan hakan, amma idan mai ba da aure da mai karba suka amince da wani kudi kasa da hakan babu laifi.

La'akari da matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar, malamin ya ce bangaren ango da bangaren amarya kan iya daidaitawa a kan kudin sadaki, amma ka da a yiwa shari'a izgilanci.

Kara karanta wannan

Saudiya ta yanke alakar diflomasiyya da Isra'ila, ta bukaci a ba 'yancin Falasdinu

Malami ya soki tsadar sadakin aure

A wani labarin, mun ruwaito cewa darajar kudin Najeriya (Naira) ta rugurguzo kasa yayin da dalar Amurka ta kara tsada inda yanzu ake musayar kudin a kan N1,639.41/$1.

A ranar Alhamis 5 ga watan Satumba ne aka ce darajar Naira ta ragu da N34 idan aka kwatanta da farashin da aka yi cinikin kowace dala daya a kan N1,606 ranar Laraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.