Kano: PDP na Tsaka da Kokarin Warware Rikicinta, 'Yan Jam'iyyar Sun Koma APC

Kano: PDP na Tsaka da Kokarin Warware Rikicinta, 'Yan Jam'iyyar Sun Koma APC

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin ya karbi sababbin masu tuban siyasa da su ka koma jam'iyyarsa ta APC
  • A ziyarar da su ka kai wa Barau har Abuja, wasu 'yan PDP, NNPP da mata masu tafiyar Kwankwasiyya sun bar siyasar iyayen gidansu
  • Sanata Barau ya bayyana jin dadin yadda yan siyasar na Kano su ke rungumar APC da ke mulki da rinjaye a majalisar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin ya sake karbar wasu manyan yan siyasa a Kano.

Jiga jigan PDP da ke gidan marigayi Ghali Umar Na'abba karkashin jagorancin Alhaji Ibrahim Tigaho ne su ka sauya sheka.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: Majalisar amintattun PDP ta shiga ganawar gaggawa

Barau
Wasu yan NNPP, PDP sun koma APC a Kano Horo: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Barak I. Jibrin ya bayyana farin cikinsa kan yadda su ka amince da akidar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barau ya tarbi 'yan NNPP zuwa APC

Mataimakin shugaban majalisa, Barau Jibrin ya bayyana jin dadin yadda karin yan NNPP a karamar hukumar Ajingi su ka koma APC. Daga cikin wadanda su ka rungumi jam'iyyar Bola Ahmed Tinubu daga NNPP akwai Sabo Sange, Danjummai Isah Ajingi da Nura Arma.

APC: Kungiyar mata ta bi Barau Jibrin

Wata kungiyar matan Kwankwasiyya da ake kira da matan mu a yau ta yi watsi da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso inda su ka tsunduma tafiyar Barau I Jibrin na APC.

Hajiya Zulai Abdullahi Bebeji ce ta jagoranci matan a ziyarar da su kai wa mataimakin shugaban majalisar a Abuja, inda su ka bayyana ficewar su daga NNPP.

Kara karanta wannan

Jiga jigan NNPP a jihohi 5 sun shiga matsala, an fara bincikensu

Wasu sun fara tsorata da Barau

A baya kun ji cewa wasu masu goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya sun fara bayyana fargaba kan yadda yan jam'iyyar NNPP ke tururuwa zuwa APC ta hannun Barau Jibrin.

Sai dai a gefe guda kuma an soki yadda mataimakin shugaban majalisar ya mayar da hankalinsa kan siyasa maimakon gudanar da aikinsa na majalisa da aka zabe shi ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.