Shugaban Majalisa Ya Yabi Tinubu bayan Daukar Kwakkwaran Matakin Inganta Ilimi

Shugaban Majalisa Ya Yabi Tinubu bayan Daukar Kwakkwaran Matakin Inganta Ilimi

  • Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Abbas ya yaba da matakin da gwamnatin tarayya, karkashin Bola Tinubu ta dauka kan ilimi
  • Wannan ya biyo bayan amincewar da shugaban kasa ya yi na daga likkafar kwalejin ilimi da ke garin Zaria zuwa jami'ar ilimi
  • Rt. Hon. Abbas ya ce matakin ya zo a gabar da ake bukatar bunkasa ilimi, kuma wannan dama ce musamman ga mutanen Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajuddeen Abbas ya ji dadin yadda gwamnatin Bola Tinubu ta daga likkafar kwalejin ilimi da ke Zaria.

Kakakin majalisar ya ce matakin daga likkafar kwalejin ta kara fito da shaukin gwamnatin kasar nan na cicciba ilimi a matakai da dama.

Kara karanta wannan

Bayan tallafin biliyoyi, gwamnatin Borno ta fitar da gudunmawar ambaliya da ta samu

Abbas
Kakakin majalisa ya yaba da daukaka likkafar FCE Zaria Hoto: Abbas Tajuddeen
Asali: Facebook

A sanarwar da Hon. Abbas ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce shi kansa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na son inganta ilimin mazauna kasar nan domin ciyar da su gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daukaka darajar FCE ya dace" - Shugaban majalisa

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa matakin da shugaban kasa ya dauka na daka likkafar FCE Zaria ya dace da tsarin ci gaban ilimi.

Rt. Hon. Tajuddeen Abbas ya taya gwamnan Kaduna, Uba Sani da sauran mazauna jihar murna bisa lamarin da ya kira da gagarumin ci gaba a bangaren ilimi.

Hon. Abbas ya fadi muhimmancin jami'ar ilimi

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Rt. Hon. Tajuddeen Abbas ya bayyana daga darajar kwalejin ilimi ta Zaria da wani mataki da zai zurfafa ilimin koyar wa.

Ya ce yanzu dalibai daga Zaria da kewaye za su samu saukin karatun jami'a a fannin malanta.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Yan majalisar dattawa sun ziyarci Borno, sun mika tallafin N74m

Shugaban majalisa ya koka kan garkuwa da mutane

A baya mun kawo labarin cewa kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajuddeen Abbas ya yi takaicin yadda yan bindiga da sauran yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka.

Koken ya biyo bayan yadda yan ta'addan suka shiga wani asibiti a Kaduna, inda su ka kwashe jami'an lafiya da marasa lafiya da ba a bayyana adadinsu ba, ba tare da sun samu cikas ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.