NECO 2024: Ɗalibai Sun Samu Gagarumar Nasara, Fiye da 60% Sun Ci Turanci da Lissafi
- Hukumar jarrabawar NECO ta fitar da sanarwa a kan sakamakon jarrabawar bana ta gama sakandare a yau Alhamis
- An ruwaito cewa dalibai da dama sun samu gagarumar nasara inda sama da 60% cikinsu suka yi zalaƙa a Turanci da Lissafi
- Farfesa Dantani Ibrahim Wushiwushi ne ya bayyana yadda sakamakon ya fito a hedikwatar NECO a birnin Minna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Hukumar jarrabawar NECO ta yi karin haske bayan sakin sakamakon jarrabawar na shekarar 2024.
Hukumar NECO ta ce a shekarar 2024, mafi yawan ɗaliban da suka rubuta jarrabawar sun samu Turanci da Lissafi.
Leadership ta wallafa cewa shugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushiwushi ne ya fitar da sanarwar a jihar Neja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NECO: Dalibai 60% sun ci Turanci da Lissafi
Hukumar NECO ta bayyana cewa a jarrabawar shekarar 2024 dalibai kashi 60.55% ne suka ci darusan Turanci da Lissafi.
Rahotanni sun nuna cewa dalibai kashi 60.55% din sun samu darusa biyar da ake buƙata idan aka hada da cin Turanci da Lissafi da suka yi.
Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ya ce dalibai da suka ci darusa biyar ba tare da lura da Turanci ko Lissafi ba sun kai kashi 83.90%.
Satar amsa ta ragu a jarrabawar NECO
Tribune ta wallafa cewa shugaban hukumar ya tabbatar da cewa a wannan karon an samu raguwar satar amsa da kashi 30.1% a kan abin da ya faru a 2023.
Ya kuma tabbatar da cewa za a gayyaci makarantun da aka samu da satar amsa domin yin bayani a hedikwatar hukumar.
Farfesa Dantani Ibrahim Wushiwushi ya yi kira ga dukkan dalibai da suka rubuta jarrabawar a bana da su ziyarci shafin yanar gizon hukumar domin duba sakamakonsu.
Yadda za a duba sakamakon NECO
A wani rahoton, kun ji cewa wadanda suka zana jarabawar NECO ta 2024 za su iya duba sakamakonsu ta hanyar ziyartar shafin hukumar na yanar gizo.
Daliban da suka zana NECO kuma suke son duba sakamakonsu, za su yi amfani da lambar rajista, lambar sirri da shekarar jarrabawar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng