Girgizar Kasa a Abuja: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Matakan da Ta Dauka

Girgizar Kasa a Abuja: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Matakan da Ta Dauka

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta dauki matakai da za su taimaka wajen dakile duk wata girgizar kasa da ka iya afkuwa a Abuja
  • Ministan kimiyya, kirkire-kirkire da fasaha, Uche Nnaji ya ce tuni gwamnatin ta fara sanya ido da kuma nazarin motsin kasa a sassan Abuja
  • Hakazalika, an kafa wani kwamitin wucin gadi da zai wayar da mutane kan matakan da za su dauka lokacin girgizar da kuma bayan ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi karin haske kan karamar girgizar kasa da aka samu a wasu sassa na babban birnin tarayya Abuja.

Bayan karamar girgizar da aka samu na kwanaki hudu a jere, gwamnatin tarayyar ta ce ta fara sanya ido da kuma nazarin motsin kasa a Abuja da kewaye.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na shirin kare hakkin yan Najeriya, za ta yaki masu tauye mudu

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan karamar girgizar kasar da ta afku a Abuja
Gwamnatin tarayya ta ce ta dauki mataki na dakile girgizar kasa a Abuja. Hoto: @ChiefUcheNnaji
Asali: Twitter

Matakan dakile girgizar kasa

Ministan kimiyya, kirkire-kirkire da fasaha, Uche Nnaji ya bayyana hakan a taron manema labarai na gaggawa a Abuja inji rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Uche Nnaji ya bayyana cewa gwamnati ta dauki matakan sa ido da nazarin motsin kasar ne domin dakile duk wata girgizar kasa da ka iya afkuwa a Abuja.

Hakazalika, ministan ya sanar da cewa nan ba da dadewa ba gwamnati za ta aiwatar da matakan dakile hadurran girgizar kasa a fadin kasar.

Ministan ya ce:

“A halin yanzu gwamnati tana aiki tare da nazarin cikakkun bayanai daga cibiyoyinta na nazarin girgizar kasa domin ba da shawarwari masu dacewa kan lamarin.

Girgizar kasa: Gwamnati ta kafa kwamiti

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an kafa kwamitin wucin gadi kan shirin ba da agajin gaggawa na girgizar kasa a wasu sassa na babban birnin tarayya (FCT).

Kara karanta wannan

Yadda mutane sama da 100 su ka rasu a manyan iftila'I 4 a Arewacin Najeriya

Babban darakta na sashen ba da agajin gaggawa na Abuja (FEMD), Injiniya Abdulrahman Mohammed ne ya sanar da hakan bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki.

Mohammed ya ce kwamitin wucin gadin zai wayar da kan mazauna Abuja kan matakan da za su dauka a lokacin girgizar kasar da kuma bayan ta.

An samu girgizar kasa a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa a cikin makon da ya gabata ne aka samu rahotannin afkuwar karamar girgizar kasa a wasu yankunan Maitama, Katampe, da Mpape.

Karamar girgizar kasar ta baya-bayan nan ta afku tare da kara mai karfi da kuma jijjigar kasa, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankunan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.