Wani Matashi Ya 'Kashe' Budurwar da Zai Aura Naja'atu Ahmad a Jihar Kano
- Ƴan sanda sun kama wani matashi, Abubakar Kurna da ake zargi da kashe budurwar da zai aura a jihar Kano
- Kotun majistire mai zama a Nomansland ta ba da umarnin a garƙame shi a gidan gyaran hali daga nan zuwa Nuwamba
- A wata ƙarar kuma kotun ta ɗaure wasu mutum biyu a gidan gyaran hali na tsawon shekaru shida kan saida bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ta cafke wani matashi, Abubakar Kurna bisa zarginsa da kashe budurwar da zai aura, Naja'atu Ahmad.
Ƴan sandan sun gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun majistire mai zama a Nomansland a ƙaramar hukumar Fagge ta jihar Kano.
Kotu ta bada umarnin garƙame Abubakar
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa alkalin kotun, mai shari'a Huda Haruna ya ba da umarnin a tsare Abubakar a gidan gyaran hali zuwa ranar 21 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alƙalin ya ɗauki wannan matakin ne saboda kotun ba ta hurumin sauraron shari'a mai girma irin wannan.
Kano: Kotu ta ɗaure wasu mutum 2
A wata ƙarar kuma kotun ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan gyaran hali bisa kama su da laifin sayar da makamai ba bisa ƙa'ida ba.
Mai shari’a Hajara Shafi’u Hamza da ta jagoranci shari'ar, ta daure su a gidan yari na shekaru shida bisa laifin sata da sayar da bindiga kirar A-K47.
Tun farko dai an gurfanar da Murray Modelo da Ejike Igwe bisa tuhume-tuhume uku da suka haɗa ɗa haɗa baki, mallaka da sayar da bindiga ta haramtacciyar hanya.
Bayan gamsuwa da hujjojin masu gabatar da ƙara, kotun ta ɗaure su shekara shida a gidan maza amma ta ba kowane ɗaya zaɓin biyan tarar N50,000.
Kaduna: Kotu ta garƙame tsohon alkali
A wani rahoton kuma wani tsohon alkalin kotun shari'ar Musulunci ya shiga hannu kan zargin cin zarafin matar aure da ta ke makauniya
Wanda ake zargin, Mahmud Shehu an gurfanar da shi a gaban kotun majistare da ke Zaria a jihar Kaduna, inda aka umarci a tsare shi a gidan yari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng