Hotuna: Yadda Rundunar Sojin Sama Ta Fara Jigilar Kayan Aikin Zaben Gwamnan Edo

Hotuna: Yadda Rundunar Sojin Sama Ta Fara Jigilar Kayan Aikin Zaben Gwamnan Edo

  • Shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar Edo ya fara kankama yayin da aka fara jigilar kayayyakin zaben daga Abuja
  • Rundunar sojin saman Najeriya ce ta sanar da cewa ta fara jigilar muhimman kayayyakin zaben kamar yadda ta saba yi
  • Rundunar ta ce fara jigilar kayan tun yanzu zai ba hukumar zabe mai zaman kanta damar shiryawa da yin aiki cikin lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rundunar sojin saman Najeriya ta fara jigilar kayayyakin zabe na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) zuwa Benin, babban birnin jihar Edo.

Wannan ci gaban ya zo ne gabanin zaben gwamna jihar ta Edo da hukumar INEC ta shirya gudanarwa a ranar 21 ga Satumba, 2024.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa: Atiku ya ziyarci Maiduguri, ya ba da gagarumar gudunmawa

Rundunar sojin saman Najeriya ta yi magana kan shirin zaben gwamnan Edo
Rundunar sojin saman Najeriya ta fara jigilar kayayyakin zaben gwamnan Edo. Hoto: @NigAirForce
Asali: Twitter

Edo: An fara jigilar kayan zaben gwamna

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwa daga mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar, Kabiru Ali wadda aka wallafa a shafin rundunar na Facebook a ranar Larabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kabiru Ali ya ce ta hanyar fara jigilar kayan tun yanzu ne zai ba hukumar INEC damar shiryawa zaben da wuri da kuma gudanar da shi cikin kwanciyar hankali.

"A yau 18 ga watan Satumban 2024 ne rundunar sojojin saman Najeriya ta fara jigilar kayayyakin zabe na hukumar INEC a shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Edo."

- A cewar sanarwar.

Kawancen sojoji da INEC a zaben Edo

Sanarwar ta kuma bayyana cewa fara wannan jigilar wani cika alkawari ne da babban hafsan sojan sama (CAS), Air Marshal Hasan Bala Abubakar ya yi ga INEC.

Kabiru Ali ya rahoto cewa Air Marshal Hasan ya gana da shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu inda shi (CAS) ya ba hukumar tabbacin jigilar kayan zaben a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Sokoto: Mummunar gobara ta babbake ofisoshi 6 a hedikwatar 'yan sandan Najeriya

"Wannan jigilar kayayyakin zaben na nuna aniyar rundunar sojin saman Najeriya na cika aikinta da kundin tsarin mulki ya ba ta na ba da agajin soji ga hukumomin farar hula."

- A cewar sanarwar.

Duba hotunan a nan kasa:

Muhimman abubuwa a kan Ighodalo

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta tsayar da Barista Asue Ighodalo a matsayin dan takararta na zaben sabon gwamnan jihar Edo.

Ighodalo ya kasance kwararren lauya kuma masanin tattalin arziki, kamar yadda muka tattaro abubuwa biyar game da dan takarar na PDP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.