Tsadar Fetur: 'Yan Majalisar Tarayya Sun Ba Gwamnatin Tinubu Shawara

Tsadar Fetur: 'Yan Majalisar Tarayya Sun Ba Gwamnatin Tinubu Shawara

  • Ƴan majalisa marasa rinjaye na majalisar wakilan tarayya sun koka kan tsadar da man fetur ya yi a ƙasar nan
  • Ƙingiyar marasa rinjayen ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta duba yiwuwar rage farashin fetur
  • Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa sun damu matuƙa bayan da kamfanin NNPCL ya sanar da sabon farashi
  • A wata sanarwa, 'yan majalisar sun nuna rashin jin dadinsu da ganin yadda fetur yi tsada ana cikin kuncin rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar masara rinjaye na majalisar wakilai ta yi magana kan tsadar farashin man fetur da ake fama da ita a ƙasar nan.

Ƴan majalisar marasa rinjaye sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta sake nazari kan farashin man fetur ta hanyar duba yiwuwar rage shi domin hana ci gaba da shan wahalar da ake yi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaba a APC ya caccaki Tinubu, ya fadi yadda Abacha ya yi masa fintinkau

'Yan majalisa sun koka kan farashin fetur
Marasa rinjaye na majalisar wakilai sun bukaci gwamnati ta rage farashin fetur Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Ƴan majalisa sun koka kan tsadar fetur

Jaridar TheCable ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Kingsley Chinda ya fitar a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kingsley Chinda ya bayyana cewa masu matsakaicin ƙarfi na ji a jika saboda tsadar fetur a halin yanzu, rahoton jaridar PM News ya tabbatar.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa sun damu matuƙa bayan sanarwar da kamfanin NNPCL ya yi dangane da sabon farashin man fetur da aka samo daga matatar Dangote.

Ƴan majalisa sun ba gwamnati shawara

"Wannan farashin ba abin da za a yarda da shi ba ne musamman duba da cewa fetur ɗin nan a cikin gida ake tace shi."
"Ya kamata farashin fetur da aka tace a cikin gida ya yi ƙasa da wanda aka shigo da shi daga waje domin ba a biya masa kuɗaɗen haraji da sauransu ba."

Kara karanta wannan

NMA ta hango wata matsala bayan ambaliya a Maiduguri, ta ba da mafita

"Duk wani farashin fetur wanda bai yi la'akari da waɗannan abubuwan ba, an shirya shi ne kawai domin a muzgunawa ƴan Najeriya musamman a lokacin da talaka ke shan wuya kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi."
"Muna kira ga ɓangaren zartaswa da sauran hukumomin da abin ya shafa da masu ruwa da tsaki da su gaggauta yin duba kan wannan farashin ta yadda ba za a ƙaƙabawa ƴan Najeriya farashin fetur wanda ba adalci a cikinsa ba."

- Hon. Kingsley Chinda

Lauya ya caccaki NNPCL kan farashin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen lauyan nan ɗan fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Femi Falana, ya yi magana kan farashin man feturin matatar Ɗangote.

Femi Falana (SAN) ya bayyana cewa a tsarin doka, haramun ne kamfanin mai na kasa NNPCL ya tsoma baki ko ya tsaida farashin man fetur da matatar Ɗangote ta tace.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng