Tambuwal: Gwamnatin Sokoto Ta Fara Binciken Tsohon Gwamna kan Zargin Satar N16bn

Tambuwal: Gwamnatin Sokoto Ta Fara Binciken Tsohon Gwamna kan Zargin Satar N16bn

  • Gwamnatin Sokoto ta waiwayi tsohon gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal inda za ta fara bincikensa kan zargin karkatar da N16.1bn
  • Kwamitin shari'ar da aka dorawa alhakin binciken gwamnatin Tambuwal ya ce zai gano inda aka kai kudin hannayen jarin jihar Sokoto
  • An rahoto cewa ana zargin Tambuwal ya karkatar da kudin bayan sayar da hannayen jarin jihar a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Gwamnatin Sokoto ta shigar da kara gaban kwamitin shari'a na jihar kan tsohuwar gwamnatin Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

Gwamnatin Sokoto na zargin Sanata Aminu Waziri Tambuwal da karkatar da Naira biliyan 16.1 ta hannun kamfanin saka hannun jari na jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ba da tallafin N100m ga wadanda ambaliya ta shafa a Maiduguri

Gwamnatin Sokoto na zargin Aminu Waziri Tambuwal ya karkatar da N16.1bn
Gwamnatin Sokoto ta soma bincike kan zargin karkatar da N16.1bn a gwamnatin Tambuwal. Hoto: @AWTambuwal
Asali: Twitter

Lauyan kwamitin shari'ar, Amanzi Amanzi ya bayyana hakan a ranar Talata jim kadan bayan da aka kammala zama kan shigar da karar, inji jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi Tambuwal da karkatar da N16bn a Sokoto

Amanzi Amanzi, ya ce ana zargin gwamnatin Tambuwal ta karkatar da kudaden ne bayan da aka sayar da hannayen jarin gwamnati a tsakanin shekarar 2018-2023.

Lauyan bayyana cewa gwamnatin jihar Sokoto ta hannun babban sakataren jihar, Abdullahi Yabo ne ya shigar da karar gaban hukumar.

Abdullahi Yabo ya bukaci kwamitin da ya bincike yadda aka fitar da hannayen jarin da yadda aka sayar da su da kuma inda aka kai kudin.

Sokoto: Za a fara binciken gwamnatin Tambuwal

Jaridar The Punch ta rahoto Amanzi ya ce:

“Gwamnati ta bukaci a binciki yadda aka sayar da hannun jarin gwamnati ta hannun kamfanin saka hannun jari na jihar Sokoto a wani lokaci a shekarar 2018.

Kara karanta wannan

Yunwa: Wasu Gwamnonin jihohin Kudu sun fitar da tsarin wadata jama'a da abinci

“An bukaci wannan kwamiti da ya binciki yadda aka sayar da hannayen jarin da kuma inda aka kai ko yadda aka batar da kudaden da yawansu ya kai Naira Biliyan 16.1.”

Lauyan kwamitin ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar na zargin cewa an ce an karkatar da Naira Biliyan hudu ta wasu asusun sirri da na kamfanoni.

Tambuwal ya gurfana gaban kwamiti

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Aminu Tambuwal, ya gurfana a gaban wani kwamitin shari'a na jihar Sokoto da ke binciken zargin almundahana a gwamnatinsa.

A watan Yulin 2023, gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, ya kafa kwamitin binciken na mutum biyar, domin bincikar duk kadarorin gwamnati da Tambuwal ya sayar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.