NNPCL Ya Bayyana Dalilin da Ya Sa 'Yan Kasuwa ba Za Su Iya Sayen Man Dangote ba
- Kamfanin man Najeriya (NNPC) ya bayyana dalilin da ya sa ‘yan kasuwa ba za su iya sayen fetur daga matatar Dangote ba
- Mataimakin shugaban NNPC, bangaren tacewa da kasuwancin mai ya ce har yanzu farashin man Dangote bai daidaita ba
- Dapo Segun ya kara jaddada cewa a halin yanzu kamfanin NNPC ne kadai zai iya sayen fetur kai tsaye daga matatar Dangote
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya bayyana cewa ‘yan kasuwa ba za su iya shigo da mai ko sayen shi daga matatar Dangote ba.
NNPCL ya sanar da cewa har yanzu farashin man Dangote bai daidaita ba kuma man bai kai ga wadatar da zai sa har 'yan kasuwa su fara saya ba.
Dapo Segun, mataimakin shugaban zartarwa na kamfanin mai na NNPC, ya ce babu wanda aka ware daga shigo da mai inji rahoton jaridar The Cable
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takaita shigo da fetur a Najeriya
Ya ce hukumar kula da man fetur ta Najeriya (NMDPRA) aka dorawa alhakin amincewa da ba izinin shigo da man fetur a cikin kasar nan.
A cewar Segun, a koyaushe ‘yan kasuwa na neman izini daga NMDPRA domin shigo da gas, kalanzir da fetur, amma ba sa shigo da fetur saboda kasuwarsa ba ta da riba.
"Ba sa shigo da fetur saboda ba sa samun riba. Ba wai NNPCL na so ya rika yin kaka-gida ba ne a shigo da fetur, kawai dai 'yan kasuwar ba sa iya yin hakan saboda babu riba."
- Dapo Segun.
Dangane da siyan mai daga matatar Dangote, Segun ya bayyana cewa ana sayar da man Dangote a farashin kasuwa, kuma NNPC ne kadai ya ke iya sayan man a yanzu.
Man Dangote ya fi karfin 'yan kasuwa
The Sun ta rahoto jami'in na NNPC ya ce ‘yan kasuwa ba za su iya siyan man fetur kai tsaye daga Dangote ba saboda ya yi masu tsada a kan yadda kamfanin ke ba su.
"Game da matatar Dangote. Tun a baya na sanar da mutane cewa Dangote kamfani ne kuma zai sayar da fetur ne a farashin kasuwar mai ta duniya.
"A halin yanzu NNPCL ne kadai ke iya sayen mai daga Dangote saboda 'yan kasuwa ba sa iya sayensa a farashin da ya ke, ba za su samu wata riba ba."
- NNPCL
Sai dai kamfanin na NNPC ya ce idan har farashin matatar ya daidaita, to za a ga 'yan kasuwa na sayen man kai tsaye daga Dangote.
NNPCL ya fara dakon man Dangote
A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin NNPCL ya fara dakon fetur daga sabuwar matatar man Dangote da ke Legas a ranar Lahadi, 15 ga Satumba.
Mataimakin shugaban kamfanin Dangote, Devakumasr V.G. Edwin ya ba da tabbacin cewa matatar Dangote na da karfin fitar da lita miliyan 54 a kowacce rana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng