'Da Arzikinsa': Minista Ya Fadi Abin da Zai Hana Bola Tinubu Satar Kuɗin Gwamnati

'Da Arzikinsa': Minista Ya Fadi Abin da Zai Hana Bola Tinubu Satar Kuɗin Gwamnati

  • Karamin ministan matasa na kasa, Ayodele Olawande ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai saci kudin Najeriya ba
  • Ayodele Olawande ya ce Tinubu ya tashi cikin arziki da rike manyan mukamai saboda haka ba zai saka hannu domin sata ba
  • Hakan na zuwa ne bayan matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta taɓa cewa ba su na neman mulki ba ne domin satar kudin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙaramin ministan matasa na kasa ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu bai zo mulki da niyyar sata ba.

Ayodele Olawande ya bayyana dalilan da yasa shugaban kasar ba zai taba satar kudi saboda yana mulki ba.

Kara karanta wannan

'Ka da mu zargi kowa': Tinubu ya bayyana abin da ya jawo ambaliyar Maiduguri

Olawande Emmanuel Ayodele
Ministan matasa ya ce Tinubu bai zo mulki domin sata ba. Hoto: Olawande Emmanuel Ayodele
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Ministan ya fadi haka ne yayin wani taro a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Tinubu ba zai yi sata ba' inji minista

Ministan harkokin matasa, Ayodele Emmanuel Olawande ya ce Bola Tinubu ya tashi cikin kudi saboda haka ba zai yi sata ba.

Ayodele ya kara da cewa shugaban kasar ya zama Sanata kuma ya rike muƙamin gwamna wanda idan kudi yake nema ma ta ya riga ya samu.

The Guardian ta ce ministan ya kara da cewa Bola Tinubu ba talaka ba ne kuma yana da harkokin kasuwanci da dama sun riga sun tara masa kudi.

Minista ya ce a yi hakuri da Tinubu

Ministan matasa, Ayodele Olawande ya yi kira ga yan Najeriya kan su kara hakuri da tsare tsaren shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Kotu ta sake zama kan zargin tsohon Minista a Kebbi da dirkawa budurwa ciki

Ayodele Olawande ya ce Bola Tinubu ya samu kasar ne a cikin rashin daidaito kuma yana da tabbas lamura za su daidaita a gaba kadan.

Ya kuma kara da cewa suna kokari ne domin sun tabbatar da cewa duk matsayin da suke rike zai zama tarihi kuma mutane za su tuna ayyukan da suka yi.

Tinubu ya yi jaje ga jama'ar Borno

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa gwamnatin jihar Borno bisa iftila'in ambaliya a Maiduguri.

Shugaban ya bayyana takaicin halin da jama'a suka shiga bayan afkuwar ambaliyar da ta kashe rayuka, ya kuma yi magana kan kafa asusun neman taimako.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng