Ambaliyar Maiduguri: Ya na Murna Ya Tsere daga Kurkuku, Jami'an Tsaro Sun Cafke Shi
- Yan sanda a jihar Bauchi sun yi nasarar damke daya daga cikin wadanda su ka tsere daga gidan gyaran hali da ke garin Maiduguri
- Rundunar yan sandan ta ce an kama Abubakar Mohammed mai shekaru 27 da ya tsere daga kurkuku bayan ambaliya a ranar Talata
- Kotu ta tabbatar masa da laifin kisan kai, kuma ana shirin mika shi ga hukumar kula da gidajen yari domin ya ci gaba da zaman kaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - Kwanaki bayan tsere wa daga gidan yari da ke Maiduguri, yan sanda sun yi nasarar kama wani matashi da ya tsere daga kurkukun.
Ambaliyar ruwa da ta mamaye wurare da yawa a Maiduguri a jihar Borno ta lalata wurare da yawa, ciki har da gidan ajiya da gyaran hali.
A sakon da rundunar yan sandan Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook, an kama matashin mai shekaru 27 bayan samun rahoton ganinsa a Bulakara da ke jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ambaliyar Maiduguri: Yadda aka kama mai laifi
Jaridar Punch ta wallafa cewa wani mazaunin mazabar Bulakara a karamar hukumar Gubio ne ya shaida wa yan sanda cewa ya gano Abubakar Muhammad da ya gudo daga Maiduguri.
Kotu ta daure Abubakar bayan tabbatar masa da laifin kisan kai, kuma ya bi sahun wasu masu laifi da su ka gudu wadanda ake kan neman su yanzu haka.
Za a mika mai laifi garin Maiduguri
Sanarwar da kakakin rundunar yan sandan Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Talata ta ce Abubakar Muhammad ya na hannunsu.
Jami'in ya kara da cewa yanzu haka ana shirin mayar da shi Maiduguri domin ci gaba da zaman gidan kaso, tare da neman jama'a su taimaka da muhimman bayanai.
Daurarru sun tsere daga kurkukun Maiduguri
A baya kun ji cewa ambaliyar ruwa a Maiduguri ta lalata wani bangare na gidan kurkukun da ke yankin, wanda ya sa wasu daurarru su ka tsere ganin cewa kowa na ta kansa.
Hukumar kula da gidan ajiya da gyaran hali ta bayyana fargabar cewa daurarrun barazana ne ga zaman lafiyar mutanen jihar, kuma akwai yiwuwar su na dauke da makamai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng